✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata mafarauta sun shiga yaki da ’yan bindiga a Taraba

Matan sun lashi takobin kawo karshen ta'adanci a fadin jihar.

Mata mafarauta sun hada karfi da karfe da ’yan uwansu maza wajen yaki da ’yan bindigar da suka addabi Jihar Taraba.

Bincike ya gano matan aure da ’yan mata da yawa sun shiga kungiyar mafarauta, don yaki da ayyukan ’yan ta’adda a fadin jihar.

Wata mafarauciya mai suna Hauwa Lawal, ta shaida wa Aminiya cewar sun shiga kungiyar ne da nufin ba da tasu gudunmawar.

Ta ce ’yan bindiga sun kashe mazajensu da ’ya’yansu, sannan kuma sun sace ’yan mata da matan aure da yawa a Kananan Hukumomin Karim- Lamido da Gassol da kuma Bali da ke jihar.

Kazalika, ta kara da cewar hare-haren ’yan bindiga ne suka tilasta wa mata da yawa a jihar yanke hukuncin shiga kungiyar mafarauta don yaki da ta’addanci.

Kokarin da matan suke yi wajen yaki da ta’addanci a jihar ne ya sanya Kungiyar Mafarautan Jihar ta bai wa Habiba Isa shugabancin kungiyar na yankin Arewa Maso Gabashin jihar.

Jim kadan bayan nadin nata da shugaban kungiyar ya yi, Umar Muhammed Tola a Karamar Hukumar Zing, ya ce mata mafarauta sun fara kawo karfi kan yadda maza mafarauta suka mamaye bangaren.

Ta ce mata mafarauta sun taka gagarumar rawa wajen yakar ‘yan tada kayar baya na Boko Haram a Arewa Maso Gabas l, wanda ta ce a yanzu haka suna ajiye makamansu.

“Da yawanmu sun gaji farauta daga iyaye da kakanni. Wasu kuma sun shiga harkar ne don kwato jiharmu daga ta’addanci,” in ji ta.