✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata da rikon ’ya’yan kishiya

’Yar uwa ki sani shi da amana ne Allah Ya ba ki riko, zai kuma tambaye ki a kan amanar.

Musguna wa ’ya’yan kishiyoyi dai ba bakon abu ba ne a nan Arewa.

Galibi bakin kishi kan kare ne a kan yaran da ba su ji ba, ba su gani ba; su tsinci kansu saboda kiyayyar kishiyoyin mahaifiyarsu cikin tashin hankali da tsangwama, hadi da musgunawa.

Halin da wasu kishiyoyi ke jefa ’ya’yan mijinsu abin bakin ciki ne, domin za a iske uban ma an mallake shi ba ya iya tabuka komai ko cewa uffan.

Za ka ga namiji ya tara mata marasa imani kowace yaran da ta haifa kawai ta sani, don haka a yi ta cin zalin juna.

Idan ka yi magana a ce yaro ya gaggara don kawai an ga mahaifiyarsa ba ta gidan.

Jahilci da kuma yadda duniya ta koma, kowa nasa ya sani ko tsakanin ’yan uwa ciki daya babu soyayya sai kiyayya suna cikin dalilan faruwar hakan.

Sai dai kuma wasu na ganin su ma yaran ba sa girmama matan nahaifansu, abin da ke sa wasu zuciya ta debe su su aikata mummunan aiki a kansu.

Mece ce mafita?

Mata ba su fiye la’akari da cewa wannan dan mijinsu ne ba, abin da suke mayar da hankali a kai wannan yaron ko yarinya ’yar kishiya ce.

Sai dai duk wacce ke cutar da yara, akwai rashin tarbiyya da imani ko matsalar kwakwalwa a tare da ita.

Daidaita kishi ko samar da mafita abu ne mai wahala, saboda masu imanin kadan ne, duba da irin zamanin da ake ciki.

Duk da haka akwai bukatar fadakarwa, nasiha tare da ilimantarwa.

Ya ke ’yar uwa! Ki sani tsagwaron zalunci ne cutar dan da koda ke ce kika haife shi, balantana wanda ba ke ce kika haife shi ba.

Ki sani Allah (SWT) zai tambaye ki a kan amanar da aka ba ki ta kula da shi.

Idan kika mutu kina zaluntarsa bai yafe miki ba, to fa ba makawa sai kin je wuta, saboda Allah ba Ya yafe hakkin wani.

Kuma ki sani tun a nan duniya sai kin ga sakayya domin shi yaron dai ba zai ji kan ki ba idan ya girma.

Watakila ma Allah Ya yi masa sakayya a kan ’ya’yanki ke ma ki fita ki auri wani wata ta zo ta gallaza wa naki ’ya’yan.

Sannan sau tari irin wadannan yaran Allah Yana ba su nasibi a rayuwa, sai ki ga sun girma Ubangiji Ya albarkace su.

Watakila ma lokacin kin zama abar tausayi kina neman taimako. Don haka ’yar uwa ki sani shi da amana ne Allah Ya ba ki riko, zai kuma tambaye ki a kan amanar.

Ku kuma iyaye maza, wajibi ne ku kare ’ya’yanku, ku ba su kariya da kula, don ku ma Ubangiji zai tambaye ku a kan amanar da Ya ba ku.

Sannan gwamnati akwai bukatar ta sa ido ta bijiro da hanyoyi takaita irin wadannan mugayen halaye da suke cutar da yara.

Akwai bukatar fadakarwa da ilimantarwa tun daga iyaye kafin aurar da yarinya. Sannan akwai bukatar sa ido a kan yanayin zamantakewa a gidaje.

Samira Bello Shinko Imel:[email protected]