✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin wata mata da kashe kishiyarta a Bauchi

Kishiyar ta amsa cewar ita ta shaƙe Hajara har lahira.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta fara bincike kan mutuwar wata mata mai shekaru 20, Hajara Isa, wadda aka tsinci gawarta a gidan mijinta aure.

Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana cewa sun samu rahoton rasuwar matar a ranar 3 ga watan Maris, 2025.

Sai dai ya ce ’yan uwan mamaciyar suna zargi kishiyarta da hannu a mutuwarta.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Auwal Musa Muhammad, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Binciken farko ya kai ga kama kishiyar mamamciyar, mai suna Fatima Mohammed, mai shekaru 28.

Da aka tambaye ta, ta amsa cewar ta shaƙe Hajara har lahira, sannan ta zuba mata ruwan zafi da ƙone gawarta don ɓoye laifinta.

Rundunar ta bayyana cewa za a ci gaba da bincike a sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID).

Hakazalika, rundunar ta ce idan buƙatar tono gawar ta taso domin yin ƙarin bincike, za ta yi hakan don tabbatar da gaskiya.