✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata a rage tsananin kishi

Tun tuni na so in yi wannan rubutun nawa, domin yin tsokaci a kan kishi, wanda lamarin a halin yanzu ya yi matukar muni da…

Tun tuni na so in yi wannan rubutun nawa, domin yin tsokaci a kan kishi, wanda lamarin a halin yanzu ya yi matukar muni da tashin hankali a tsakanin mata ma’aurata.   Hakika abubuwan da suka wakana a ’yan kwanakin nan wanda har a kafofin yada labarai sukai ta yayata wa a kasar nan, akan rashin imanin da wasu mata ma’aurata suka aikata akan ‘ya’yan kishiyoyinsu.
Abubuwa guda uku na rashin imani da suka rikita kwakwalwa ta, akan wasu mata da suka aikita abu mafi muni akan ’ya’yan kishiyoyin su. Hakika lamarin ya yi matukar razana ni da tayar min da hankali musammanma yadda na ji wata matar aure saboda rashin imani ta yanke al”aurar jinjiri don kwanaa 23 da haihuwa, saboda kawai a kwai takaddamar kishi a tsakanin ta da uwarsa.
 Kana wasu matan biyu kishiyoyin juna su ma kishin ya kai su har suka halaka ’ya’yansu 6 ta hanyar jefa su cikin rijiya saboda takaddamar kishi da ta kaure a tsakaninsu, domin wai uwar gidan ita ta fara jefa kazar kishiyar ta a cikin rijiya, a sakamakon haka har ta kai su da aikata wannan aikin mafi muni da kuma da-na-sani a duniya da lahira.  
 Sai kuma wasu kishiyoyin guda biyu su kuma nasu aikin asshar shi ne  karairaya kafafun dan kishiyarsu suka yi tare da lakada masa dukan kawo wuka, saboda sun yi zaman kishi da uwarsa kafin mijinsu ya sake ta ta bar gidan.
Tabbas abubwannan du suka faru na tashin hankali game da ma”auratan matan nan saboda kishi to lalle lamarin abin dubawa ne da hangen nesa, da kuma tambayar kawunanmu cewa shin mai ya janyo wannan bakin kishin da mata ma’aurata suke aikata wa alhali a da iyayanmu mata ba sa iya kwatanta irin wanan rashin imani a zahiri?
Da farko dai dole in fara bayani gwargwadon fahimta ta akan shin mai ya janyo mata ma’urata suke aikata irin wanan rashin Imani da sunan kishi?  Me ya sa a halin yanzu ake yawan nuna tsananin fushi da sunan kishi har ya wuce tunanin mai tunani, da yake shi kishi iri-iri ne amma wanda mutane suka fi sani kuma muke magana akai shi ne na mata ma’aurata da suke auren miji daya.
Kishi dai wata damuwa ce da ta kan samu zuciyar mutum, ko kuma shi mutum yakan sa kansa a cikin damuwa a lokacin da yake ganin alamar zai rasa wani abu da yake matukar kauna da so, wanda idan mutum bai yi taka tsantsan ba to sai ya shiga cikin wani hali na kaka- ni- ka-yi watakila ma ya zo yana da-na- sani.   Hakazalika shi kishi wani kulli ni da ke cikin zuciya  wanda kuma ya fi kusa da kiyayya amma a lokaci guda ba ya nisa a tsakaninsa da soyayya.
Wani masanin falassafa cewa ya yi shi kishi wani abu ne da ke tsakanin soyayya da kiyayya, wanda in ya yi kasa yana da harshashin kiyayya haka kuma in ya yi sama yana zarce soyayya domin kishi wani makami ne mai karfin gaske da ke jefa harsashin kiyayya kasa ya kuma harba soyayya sama sannan kuma an ce kishi abu ne da zamani ko lokaci zai iya fayyace mana muninsa ko kyawunsa, alherinsa ko sharrinsa.
 Bayan haka shin wacce rawa magidanta suke takawa a tsakanin matansu domin kauce wa aukuwar  mugun kishi da mata suke yi a halin yanzu har ta kai su ga aikata babbban zunubi?
A nazarina da tunanina ni ina ganin na bai wa maza laifi, domin sakacin su na kasa hada kawunan matan su a wuri guda, da kuma uwa uba rashin adalci da wasu magidanta suke da shi da zarar sun auro wata matar.   Wannan rashin adalci na wasu mazajen bai tsaya  ga matan da suka  tsana ba a’a har ya gangara ga’ya’yansu, don haka daga nan sai wagegiyar kofa ta fitina ta budu a cikin gidan, sai ka ga ita matar da mijin ya fi kauna  ta samu damar cin mutuncin kishiyarta, sai ka ga ta gallaza mata har da ‘ya’yanta, wani sa’in har da cutar da su.   Saboda haka haka  ita ma ‘yar borar wacce aka fi tsana a gidan sai ta maida martini mafi muni wanda sau tari wannan martani za ka ji ya zama abin yayata wa a gari da kafofin yada labarai saboda muninsa.
Shawarata ga mata masu mummunan kishi ita ce, don Allah su daure su yi hakuri akan maganar kishiya da kishi ,domin hakika kishi ne sabubban da ke haifar musu da aikin da- na- sani wanda a karshe yakan zame musu da-na- sani a nan gidan duniya da kuma a lahira.
Don haka ku sani cewa ita maganar kishiya tun da Allah ne da kanSa Ya umarci maza da yiin aure fiye da mace daya a cikin Al’kur’ani.   Mata biyu, uku hudu amma in ku na tsoron ba za ku iya adalci ba, to, ku auri daya, (Suratul Nisa’i).
 Sannan Manzon Allah (S.A.W) ya ce, ku yi aure ku hayayyyafa domin in yi alfahari da ku a ranar gobe al-kiyama.   Don haka auren mace fiye da daya ba aibu ba ne in dai an yi don raya sunnar Manzon Allah (S.A.W).
Su kuma ’yan uwana maza ina shawartar ku da ku ji tsoron Allah, ku yi hattara ku guji gamuwar ku da Allah,  kada ku ga kamar Allah Ya ba ku ’yanci na aure da saki ku ce za ku yi yadda kuke so, domin mata amanar Allah ne a gareku.   Matarka kada ka ci amanar ta don haka ko shakka babu za ku tsaya a gaban Allah ka fuskanci shiri’a na irin zaman da kuka yi.    Yakamata mu yi koyi da yadda Manzon Allah (Saw) ya zauna da matansa, idan muka yi haka tabbas za mu samu rayuwa mai inganci da albarka, daga mu har zuri’armu.

Za a iya samun Ado Musa a lambar waya kamar haka:  08069186916