✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata 4 na mutum 1 sun haihu rana daya a sansanin ’yan gudun hijira

Gwamnatin Jihar ta ce ita za ta dauki nauyin kula da su

Wasu mata hudu da ke auren miji daya, sun haihu rana daya a wani sansanin ’yan gudun hijira da ke Jihar Borno.

Kwamishinar Mata ta Jihar, Hajiya Zuwaira Gambo ce ta bayyana hakan yayin da take bayyana koke ga kwamitin da ke bincike kan take hakkin dan Adam a ayyukan yaki da ta’addanci a Arewa maso Gabas.

A cewarta, an samu karuwar masu juna biyu da hayayyafar jarirai a sansanonin gyaran hali na Boko Haram.

Ta ce ma’aikatar ce za ta dauki gabarar kula da wadannan matan da suka haihu rana guda.

Ta kuma bayyana fargabarta kan yadda wasu mata a sansanin ke samun juna biyu da kuma haihuwar jariri kusan duk bayan wata hudu.

Bayan jawabin nata, kwamitin bisa jagorancin Mai Shari’a Abdu Aboki mai murabus, ya ce suna gudanar da binciken kan tilasta wa masu juna biyu akalla 10,000 a sansanonin zubar da ciki ne, tare da neman bahasi daga Kwamishinar.

Kwamishinar ta musanta zargin, inda ta ce ta yi mamakin bullar rahoton, domin babu kamshin gaskiya a ciki.

“Rahoton Reuters ya bani mamaki, domin sansanonin da suka fada babu wani da sojoji suka samu bayanin ya faru da shi, domin gwamnati na kula da kowa yadda ya kamata.

“Babu yadda za a yi sojoji ko wani ya ba da magungunan zubar da ciki a sansanonin gudun hijira, hasali ma babu wani soja da aka bai wa izinin shiga sansanonin sai dai wuraren shiga don gadi.

A cewarta, akwai lokacin da magidantan sansanin suka kai karar cewa ba sa so maza su dinga zuwa inda matansu suke, don haka ta yi mamakin yadda irin wadannan “mazajen masu kishi” za su kyale kowa ya taba matansu balle ta kai ga ba su maganin zubar da ciki.

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya ne kamfanin dillancin labarai na Reuters din ya rawaito cewa sojoji da ma’aikata a sansanonin gudun hijira a yankin Arewa maso Gabas na take hakkin dan adam.

Bayan bullar rahoton ne kuma gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan lamarin, don tabbatar d agaskiyar lamarin