Masu zanga-zangar neman ’yancin kai a Canberra, babban birnin Kasar Australiya, sun banka wa tsohon ginin majalisar kasar wuta.
Jami’an tsaron kasar cafke masu zanga-zangar masu yawan gaske bayan faruwar lamarin na ranar Alhamis.
- Muhimman abubuwan da suka faru a Kannywood a 2021
- Dalilin da na gudu tun kafin Taliban ta kwace mulki – Tsohon Shugaban Afghanistan
Babu wanda ya samu rauni a sanadin tashin gobarar, wadda ta kama kofofin shiga tsohon ginin, kuma daga bisani an yi nasarar kashe ta.
Lamarin ya faru ne bayan an shafe mako biyu ana tafka rikici a kasar, kamar yadda majiyar hukumomin kasar ta tabbatar.
Fira Ministan Australiya, Scott Morrison, ya yi Allah wadai da yadda rikicin ke ci gaba da kamari, yana mai cewa a baya ba haka kasar take ba.
“Wannan abin takaicin ya ba ni haushi ganin yadda ’yan kasar nan suke cinna wa wurare masu muhimmanci wuta,” inji shi.
An dai kwashe dukkan ma’aikatan da ke aiki a cikin ginin.
A yanzu ana amfani da ginin ne a matsayin gidan tarihi mai suna ‘Museum of Australian Democracy’.
A shekarar 1988 ne majalisar kasar Australiya ta sauya matsuguninta zuwa wani sabon gini da ke kusa da wannan a Capitol Hill, kafin daga baya a mayar da tsohon ginin gidan tarihi.