✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu zanga-zanga kan canjin kudi sun kona bankuna 2 a Ogun

Bankunan da aka kona su ne Union da Keystone

Wasu fusatattun matasa masu zanga-zanga a ranar Litinin sun fasa rassan bankunan Union da Keystone a garin Shagamu na Jihar Ogun.

Mutanen dai sun alakanta zanga-zangar ce da karancin sabbin kudi, kuma ta fara ne daga fadar basarake Akarigbo na Remo, Oba Babatunde Ajayi, yayin da wasu suka tare hanyoyi suna kone-kone.

Ko a ranar Juma’ar da ta gabata sai da masu zanga-zangar suka fantsama a titunan yankin Mowe kan matsalar kudin.

To sai dai a cewar wani jagoran matasa a garin, Kayode Segun-Okeowo, “matakin ya fi kama da ta’asa fiye da zanga-zanga.”

“Wannan ba zanga-zanga ba ce. Ni dan gwagwarmaya ne, na san zanga-zanga sosai. Wannan barna ce kawai. Duk wadanda suke da hannu ya kamata su bari,” kamar yadda ya shaida wa Amniya a tattaunawarsa da wakilinmu da wayar salula.

Ya kuma tabbatar da da cewa an kona bankunan kasuwanci guda biyu yayin zanga-zangar.

Kazalika, a ranar Lahadi, Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar ta yi zargin cewa akwai masu yunkurin yin amfani da matsalar rashin kudi da ta man fetur wajen tayar da zaune tsaye.

Ta kuma ce tana da bayanan sirri kan masu neman yin amfani da yanayin wajen kai wa bankuna da wasu gine-ginen gwamnati hari.

Kakakin rundunar a Jihar, Abimbola Oyeyemi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abeokuta, ranar Lahadi.