✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu zagin Buhari a fili na zuwa Aso Rock su debi girki —Adesina

Bayan sun ci mutuncin Buhari suna zuwa Aso Rock da dare su kwashi gara.

Hadimin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan Yada Labarai, Femi Adesina, ya ce yawancin mutanen da ke sukar Buhari a bainar jama’a kan je Fadar Shugaban Kasa su ci abinci da shi.

Femi Adesina ya bayyana hakan ne a bayaninsa kan sauya shekar tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani Kayode — wanda ake kira da FFK kuwa mai sukar Buhari — zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Ya ce, “A shekara shida da nake aiki da shugaban kasa na ga irin karamcinsa da yafiya masu ban mamkaki — Na sha zuwa gidansa da yamma in same shi yana cin abinci tare da mutanen da a safiyar ranar sun ci mutuncinsa da na kakanninsa a gidajen talabijin.”

Ya ce duk da cewa ana zargin Buhari da riko, yadda shugaban kasar ya karbi FFK ya karyata masu irin wadannan maganganu.

Fani-Kayode — wanda ya yi kaurin suka wajen sukar Buhari — dai na ci gaba da shan caccaka daga wurin ’yan kallo da ’yan jam’iyyar APC da PDP da ya baro, tun bayan dawowarsa APC, inda shugaban rikon jam’iyyar, Mai Mala Buni, ya kai shi Fadar Shugaban Kasa ya gana da Buhari.

A shafinsa na mako-mako, Femi Adesina ya ce Shugaba Buhari karimi ne, kuma yadda ya tarbi Fani-Kayode ya isa zama shaida a kan hakan.

“Daga makon jiya zuwa yanzu mutane na ta bankado miyagun maganganun da FFK ya yi ta yi wa duk wani mai alaka da jam’iyar APC kan abin da bai kai ya kawo ba. A wurin yawancin mutane, irin miyagun abubuwan da ya fada ba wadanda za a yafe ba ne.

“Bayan Shugaba Buhari da iyalansan da dansa Yusuf wanda Fani-Kayode ya yi wa fatar mutuwa bayan ya yi hatsari a kan babur, FKK ya ci mutuncin jam’iyyar APC da gwamnatinta da shugabanninta da kungiyoyi da ma daidaikun mutane. Ni kai na ya sha muzanta ni a rubuce-rubucensa.

“Tabbas, ya fada cewa da ya dawo APC gara ya mutu, amma a makon jiya sai ga shi ya dawo — kuma da ransa da lafiyarsa.

“Hakika ’yan APC da dama sun so ganin FFK ya dawo cikinta, kuma ga shi ya dawo a cikin martaba; Ba a mazabarsa ta Ile-Ife a Jihar Osun ba, a’a, a Fadar Shugaban Kasa kuma Shugaba Buhari ne ya karbe shi.”

A cewarsa, baya ga Fani-Kayode, Buhari ya sha karbar bakuncin mutanen da ke sukar sa tare da cin mutuncinsa a bainar jama’a, har kuma ya ci abinci tare da su.

“Nakan je gidan Buhari in same shi a kan tebur yana cin abinci tare da mutanen da a ranar da safe an gan su a gidajen talabijin suna sukar sa suna cin mutuncinsa da na kakanninsa. Yana da yafiya da dattaku da kuma son zaman lafiya.