Kawo yanzu masu zaben Sarki na Masarautar Zazzau sun kebe domin gudanar da aikinsu na zaben sabon Sarkin Zazzau kamar yadda al’ada ta tana da.
Kebewar tasu na zuwa ne washegarin ranar rasuwar Sarki na 18, Alhaji Shehu Idris, wanda ya rasu a ranar Lahadi 20 ga Satumba, 2020 bayan shekara 45 yana mulkin masarautar.
- Sarkin Zazzau: Za a yi zaman makokin kwana uku a Kaduna
- Yau za a fara rajistar tallafin kanana da matsakaitan sana’o’i
Masu zaben Sarki a Masarautar Zazzau sun hada da Wazirin Zazzau, Ibrahim Aminu; Fagacin Zazzau, Umar Mohammed; Makama Karami, Mahmood Abbas; Limamin Juma’a, Dalhat Kasim; da kuma Limamin Kona, Sani Aliyu.
Ya zuwa yanzu gidaje uku ne suka gabatar da sunayen wadanda suke neman maye gurbin sarkin.
Gidajen sarautar sun hada da gidan Katsinawa da gidan Bareberi da gidan Mallawa.
Idan masu zaben Sarki sun kammala aikinsu, za su mika sunayen wadanda suka zaba ga Gwamnatin Jihar Kaduna domin bayyana wanda Allah Ya ba wa.
Shin wa zai iya zama sabon Sarkin Zazzau?
Tuni dai aka fara hasashen wandan ke iya zama gamajin Sarki Shehu Idris.
Wadanda ake hasashen sun hada da:
- Gidan Katsinawa
- Iyan Zazzau Alhaji Muhammadu Bashir Aminu.
- Dan Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu.
- Gidan Barebari
- Yariman Zazzau Alhaji Munnir Ja’afaru.
- Dan Sarkin Zazzau Ja’afaru Dan Isiyaku.
- Gidan Mallawa
- Magajin Garin Zazzau Amb Ahmed Nuhu Bamalli.
- Dan Magajin Gari Alhaji Nuhu Bamalli.
Wasu kuma na hasashen wasu daga cikin ‘ya’yan mamacin wanda ya fito daga gidan Katsinawa:
- Turakin Zazzau Alhaji Aminu Shehu Idris.
- Ubangarin Zazzau Alhaji Bashir Shehu Idris.