Matasa 25 daga cikin masu yi wa kasa hidima a Jihar Gombe sun kamu da cutar COVID-19 wadda ake fargabar yaduwar nau’inta na Delta a Najeriya.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Gombe, Dokta Habu Dahiru, ya bayyana wa wakilinmu cewa daga cikin matasan da suka kamu da cutar akwai wata mata mai shayarwa da wasu mutum uku da ke fama da cututtukan hawan jini da kuma Asma.
- Daliban FGC Yauri 2 sun tsere daga hannun ’yan bindiga
- ’Yan bindiga na bore kan sauke sarki a Zamfara
“An gano matasan ne a lokacin da suke samun horo a Sansanin Horas da Matasa Masu Yi Wa Kasa Hidima da ke Amadan, kusan kwana biyar da suka wuce,” inji shi.
Dokta Dahiru ya bayyana cewa yawancin masu cutar sun fito ne daga jihohin da aka samu bullar nau’in Delta na cutar ta COVID-19.
“Saboda haka an dauki jininsu za a kai a yi musu gwaji domin a tabbatar ko nau’in Delta na cutar ta COVID-19 ce,” inji Kwamishinan Lafiyar.
Ya kara da cewa yawancin matasan da aka gano suna dauke da kwayar cutar ba mutanen da alamominta suke bayyana a jikinsu ba ne.
Dokta Dahiru wanda shi ne Babban Jami’in kula da wadanda aka samu da cutar a Jihar ta Gombe ya ce an riga an killace matasan da suka harbu din a Asibitin Cututtuka Masu Yaduwa da ke Kwadon, Karamar Hukumar Yamaltu/Deba ta jihar kuma suna samun sauki.
A cewarsa, bayan mako guda zuwa biyu za a sake yi musu gwaji domin sanin halin da suke ciki.
Don haka ya yi kira ga al’ummar Jihar da su ci gaba da bin matakan kariyar cutar COVID-19 da suka hada da bayar da tazara da sanya takunkumi da kuma yawaita wanke hannu.
Masu yi wa kasa hidima 1,291 ne aka yi wa gwajin cutar ta COVID-19 a Jihar Gombe.