Wata motar bas dauke da masu aikin Umrah a kasar Saudiyya ta yi kuli-kulin-kubura inda nan take mutum uku suka ce ga garinku nan.
Motar da ke dauke da masu Umarh 16 daga kasar Masar ta wuntsula ne bayan da ta yi karo da wani rakumi a kan hanyarta ta zuwa birnin Makkah domin yin ibadar.
“Karamin Ofishin Jakandanci da ke Jiddah na bibiyar hatsarin motar tare da tuntubar hukumomin Saudiyya domin tabbtar da adadin wadanda suka rasu da kuma hakikanin musabbin rasuwar tasu,” inji gwanatin Masar.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta ce mummunan hatsarin ya ritsa da maniyyatan ne a garin Tabuk mai tazarar kilomita 310 daga Makkah.
Ofishin ya kara da cewa ko da aka isa asibiti da mutanen da hatsarin ya ritsa da su, sai likitoci suka tabbatar musu da cewa uku daga cikinsu sun riga sun rasu, sauran kuma ana nan ana jinyar su.
Hatsarin na zuwa ne kwanaki kadan bayan Saudiyya ta bude iyakokin ga ’yan kasashen waje, bayan da ta rufe su a karo na biyu, saboda guje wa cutar COVID-19 wadda ke sake bazuwa.
A karon farko da cutar ta bulla a Saudiyya, kasar ta dauki makamancin matakin wanda ya kai ga takaita yawan mahajjata zuwa mutun 10,000 a shekarar 2020.