Yanzu haka gomman mutane ne suka yi wa Babban Bankin Najeriya (CBN), cikar kwari a Jihar Legas.
Mutanen na ta kokarin canja tsofaffin takardun kudadensu ne bayan umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na ci gaba da amfani da tsohuwar takardar Naira 200.
- ’Yan sanda sun dakile harin ’yan bindiga kan jami’an INEC
- An ceto jaririyar da mahaifiyarta ta jefa a masai a Kano
A cikin jawabin da ya yi wa ‘yan Najeriya a ranar Laraba, Buhari ya umarci mutane da su kai tsofaffin takardun kudinsu CBN, yayin da sabon wa’adin amfani da takardar N200 zai ci gaba har zuwa ranar 10 ga watan Afrilu.
Sai dai gwamnonin jihohin Kano da Kaduna sun soki umarnin na Buhari, inda suka ce yana kokarin kai jam’iyyar tasu kasa bayan cikar burinsa na zama shugaban kasa.
Gwamnan Jihar Kaduna, ya bayar da umarnin ci gaba da amfani da takardun kudin N500 da N1000 a jihar har zuwa lokacin da kotun koli za ta yanke hukunci kan karar da suka shigar da Gwamnatin Tarayya.
Sai dai a halin da ake ciki jami’an CBN na fama da mutane kan yadda za su sauya tsofaffin kudadensu.
Hakan ya sa suka umarci mutane su kai kudin bankunan kasuwanci amma mutane suka yi burus da umarnin jami’an.
Wani mai amfani da kafafen sada zumunta mai suna Malik, ya ce dan uwansa ya je ofishin CBN da ke Marina da misalin karfe 6 na safiyar Juma’a, amma shi ne na 420 a layin mutanen da za su sauya kudadensu.
Ya ce mutane na shan wahala kafin samun lambobin musayar kudin a shafin CBN na Intanet da ta bude.