Tsohon Sarkin Kano, Halifa Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa masu kiran a raba Najeriya suna yin babban kuskure.
Halifa Muhammadu Sanusi II ya bayyana haka ne a wajen wani biki a Legas wanda aka shirya domin taya shi murnar cika shekara 60 a duniya.
- Dalilin da muke bambanta masu kudi da talakawa a aikinmu – Hisbah
- Akwai ’yan Najeriya 322,000 da ke gudun hijira a makwabtan kasashe – Minista
Halifa Sanusi II, ya ce akwai bukatar kasar nan ta ci gaba da kasancewa a dunkule sannan a gudanar da mulki cikin adalci.
Tsohon Sarkin ya kuma nuna takaicinsa a kan yadda wadansu shugabanni a Najeriya ba sa mayar da hankali wajen ilimintar da al’umma.
Halifa Sanusi II ya ce bai wa bangaren ilimi musamman na ’ya’ya mata muhimmanci shi ne zai kawo ci gaban kasa da kuma bunkasar tattalin arziki.
A lokacin bikin, abokan Halifa Muhammadu Sanusi sun tara makudan kudi domin tallafa wa ilimin ’ya’ya mata a Najeriya.
Tsohon Sarkin na Kano ya kaddamar da littafin makalolin da ya rubuta wanda kudin da aka tara su wajen sayensu ne za a yi amfani da su wajen tallafa wa ilimin.
Ya kuma yi amfani da matsayinsa na Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a kan Muradun Ci-gaba (SDGs) wajen nanata bukatar masu hannu da shuni a kasar nan su tallafa wa ilimi musamman a yankunan karkara.
Gwamnoni shida ne suka halarci bikin ciki har da na Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i da takwaransa na Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu.
Attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Mista Godwin Emefele da shugabannin bankunan kasuwanci da wadansu sarakunan gargajiya duk sun halarci bikin.