Wadansu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun kashe Ardon Gundumar Richifa da ke karamar Hukumar Soba a Jihar Kaduna.
A ranar Talata 19 ga Satumba da dare ne masu satar mutanen suka yi wa gidan Ardon Alhaji Shehu Abdullkarim Buderi da ke Bakuntu Unguwar Fulani da ke yankin Soba dirar mikiya suka sace shi, kuma bayan ya kwashe kwanaki a hannunsu ne suka kashe shi, suka kuma harbi dan kanensa mai suna Bello Haruna.
kanen Ardon, Alhaji Haruna Abdulkarim Fulana ya shaida wa Aminiya cewa a ranar Talatar da misalin karfe 12:05 na dare, suna kwace sai suka ji karar bindiga na tashi a kofar dakin yayansa, shi kuma yana ta salati. Ya ce haka ya daure na nufi dakin yayansa, maharan suka hasko shi da fitila suka auna shi da bindiga, amma yai ce musu ba ya dauke da komai, daga baya dan uwan nasa ya fito suka tafi da shi, kuma sun kai mutum 20, duk suna dauke da bindigogi kamar yaki.
Ya ce, “Da za su tafi da yayana ne sai dana Bello da ’yan uwansa suka bi su a baya, ni kuma na tafi makwabta neman gudunmawa. To ashe sun kwanta a gonaki sai suka bude musu wuta suka harbi Bello a duwawu, suka tafi da yayana, na dauki Bello na kai asibiti. Washegari da yamma sai na ji an ce wadanda suka sace yayana sun bugo wa dan Sarkin Richifa mai suna Ibrahim Fele waya cewa a ba su Naira miliyan biyar.”
Ya ce yana asibitin, sai Sarkinsu ya aiki Ibrahim Fele cewa lallai a samu kudin a bayar don kada su hallaka shi. Daga nan sai ’yan uwansa suka ba da Naira dubu 500 a kai musu a ranar Alhamis, “Kuma a zatona a ranar suka kashe shi domin tsintar gawar aka yi ta fara rubewa, kuma abin mamaki ana hanyar kai kudin a cikin mota tare da Ibrahim Fele sai ya ce a tsaya ya fita daga motar, can ya dawo ya ce wadanda za a kai wa kudin sun bugo masa waya cewa sun ga an cika mota da mutane, ba su ce a je da kowa ba sai shi kadai. Don haka kowa ya sauka ya koma, haka aka sauka aka bar shi daga shi sai direban da yake tuka motar suka tafi,” inji shi.
Babban dan marigayin mai suna Abdullahi Ardo ya ce daga farko masu satar mutanen sun nemi a kai musu Naira miliyan bakwai ne. Kuma ya ce, Ibrahim Fele wanda da shi barayin suke magana, ya kai musu rabin miliyan a ranar Alhamis, “Bayan Sallar Isha’i sai na kira wayar Babana sai Ibrahim Fele ya daga wayar, ya ce bari ya ba Babana, da yaba shi wayar sai ya ce kudin da aka kai musu ba su isa ba, kudin cin abinci ne. Muna jin ranar da aka kai musu kudin suka kashe mahaifina, sauran bayani abokin Babana zai yi muku domin su ne suke waya da shi lokacin da yake can da shirya yadda za a kai kudin,” inji shi.
kanen Sarkin Richifa kuma babban abokin marigayin, mai suna Abubakar Audu, ya ce shi da marigayin abokai ne tun suna yara. “Gaskiya wannan lamari yana da daure kai, domin muna cikin tashin hankali tun daga ranar da aka ce an tafi da shi har zuwa yau. Wanda ya tuka motar kai kudin kanena ne uwa daya uba daya, mai suna Shu’aibu Abdullahi. Bayan sun tafikai kudin da Sallar Isha’i na buga musu waya inji yadda aka yi, sai suka ce kudin da aka kai ya yi kadan, kudin abincin da suka ba shi ne. Suka ce su da suka nemi Naira miliyan bakwai yaya za a kai musu Naira dubu 500 saboda haka da wanda ya kawo kudin da Ardon duk sun hada sun rike suna neman Naira miliyan 15. Sai suka saki direban motar sauran kuma sai mun kai kudin haka muka rabu da su. To da gari ya waye sai na tafi Zariya domin duba wanda aka harba, sai kanena ya bugo waya cewa in yi maza in fito kauyen domin mutanen nan sun harbi wani a gabansa, amma shi yana hanyar dawowa ya yi kusan fitowa daga dajin, sai na ce mu hadu a Zariya a asibitin da aka kwantar da Bello,” inji shi.
Ya ce yana kan babur kafin ya isa Zariya sai Sarkin Richifa ya bugo masa waya cewa dansa da mutanen suka rike ya gudo yana gida. Sai ya kira kanensa Shu’aibu da suka kai kudin ya gaya masa cewa Sarki ya bugo waya cewa Ibrahim ya gudo saboda haka ya yi maza ya dawo don kada su biyo sawu.
Malam Abubakar, ya ce wadansu masu aiki a gonar Alhaji Kabiru ne suka ga gawar Ardon, suka gaya wa masu gonar su kuma suka sanar da ’yan sanda, aka sanar da Sarkin.
Kantoman karamar Hukumar Soba, Alhaji Nasiru Abdu Banki ya ce sun ziyarci gidan Ardon kuma sun hada gwiwa da jami’an tsaro domin kara daukar matakin kare rayuka da dukiyar jama’ar yankin, kuma sun tallafa wa iyalansu domin kula da wanda aka harba.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduda ASP Mukhtar Hussaini Aliyu ta waya har sau uku amma bai dauki wayar ba kuma bai amsa sakon tes da ya aike masa ba.