Wasu daga cikin masu neman sarautar Sarkin Sudan na Kwantagora a Jihar Neja sun yi fatali da sakamakon zaben sabon sarkin, suna zargin cewa an fi karkata ga wani dan takara.
Wakilinmu ya rawaito cewa kimanin mutum 47 ne suka nuna sha’awarsu ta zama sabon sarkin.
- Yadda rikicin Boko Haram ya lakume rayukan yara 300,000 a Arewa maso Gabas
- Abin Da Ya Sa Mutane Ke Gudun Riga-Kafin COVID-19
Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautun Gargajiya na Jihar Neja, Barista Abdulmalik Sarkin Daji shi ne ya sanar da sakamakon zaben da ya gudana ranar Lahadi.
Ya sanar da shi ne ta gidan rediyon Landmark da ke garin na Kwantagora, inda ya bayyana Muhammad Barau a matsayin wanda ya sami kuri’u mafi rinjaye, amma ya ce Gwamnan Jihar, Abubakar Sani Bello ne yake da wuka da naman sanar da sabon Sarki daga cikin ’yan takarar.
To sai dai daya daga cikin ’yan takarar, Barista Mika Anache a ranar Litinin ya yi kira da a soke zaben, inda ya zargi kwamitin zaben da kuma Ma’aikatar Kananan Hukumomin da kauce ka’ida yayin aikin.
Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar da ta tilasta wa masu zaben sarkin su sake gudanar da zaben sannan kuma ta cire Kwamishinan na Kananan Hukumomi saboda nuna rashin kwarewa wajen tafiyar da al’amuran masarautar.
Mai karar ya kuma aike da kwafin korafin ga Kakakin Majalisar Dokokin Jihar da Etsu Nupe da shugaban DSS da tsoffin Shubannin Kasa Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar da kuma shugaban masu zaben sarkin na masarautar, Alhaji Shehu Yusuf Galadima.
Barista Anache ya zargi masu zabar sarkin da kuma ma’aikatar da hana ’yan takarar shiga wajen da ake gudanar da zaben.
Sai dai ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, dukkan wadanda aka mika wa kwafin takardar korafin ba su kai ga mayar da martani a kai ba.