✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu neman sabbin kudi sun tare kofar CBN a Abuja

’Yan Najeriya da suka je ajiye tsoffin takarudun kudade sun hana shiga ko fita ta kofar shiga ofishin Babban Bankin Najeria (CBN) a Abuja.

’Yan Najeriya da suka je ajiye tsoffin takarudun kudade sun hana shiga ko fita ta kofar shiga ofishin Babban Bankin Najeria (CBN) a Abuja.

Fusatattun mutanen sun hana ma’aikata da ma baki shiga ko fita daga ofisihn na CBN da ke yankin Garki a Abuja na tsawon awanni, sai da aka kai ruwa rana.

Mutanen dai sun je ofishin na CBN da nufin ajiye tsoffin kudadensu kamar yadda bankin a tsara, amma sai wankin hula ke neman kaiwa dare, abin da suke zaton za a yi cikin kankanin lokaci, sai ga shi sun yi sa’o’i babu biyan bukata.

Wata daga cikinsu, Folashade Bello, ta ce “Mun zo ajiye tsoffin kudadenmu yadda CBN ya ce, amma abin takaici, shafin din da suka bude domin hakan ba ya aiki, sannan babu wanda ya fito ya yi mana bayani ko ya ba mu fom mu cike.

“Wahalar da muke sha ta wuce misali, wahala muka sha kafin mu samu wannan kudin, amma kuma a ce sai mun wahala kafin mu taba kudinmu.”

Shi kuma wani mai suna David, cewa ya yi, “Mun kwashe sa’o’i a nan ba mu samu komai ba. Sun ce mu rubuta sunayenmu, amma har yanzu babu wani labari.

“Shafin nasu ba ya aiki kuma babu wanda ya kawo mana fom mu cike.

“Wasunmu dage Suleja suka zo suna zaton za su ajiye tsoffin kudadensu su koma gida, amma tsugune ba ta kare ba. Sai ka wahala kafin ka ajiye tsoffin kudinka, sai ka wahala ka samu sabbi.”

Hakan ne ya fusata su, suka tare kofar shiga bankin na tsawon awanni.

Aminiya ta gano daga baya rundanar ’yan sanda ta birnin tarayya ta shawo kan mutanen, bayan sun tare ofishin na CBN na tsawon awanni.