’Yan Najeriya da suka je ajiye tsoffin takarudun kudade sun hana shiga ko fita ta kofar shiga ofishin Babban Bankin Najeria (CBN) a Abuja.
Fusatattun mutanen sun hana ma’aikata da ma baki shiga ko fita daga ofisihn na CBN da ke yankin Garki a Abuja na tsawon awanni, sai da aka kai ruwa rana.
- Gwamnatin Kano ta lashe amanta kan hukunta masu kin karbar tsoffin kudi
- Hukuncin Karin kudin da masu POS ke yi —Sheikh Ibrahim Khalil
Mutanen dai sun je ofishin na CBN da nufin ajiye tsoffin kudadensu kamar yadda bankin a tsara, amma sai wankin hula ke neman kaiwa dare, abin da suke zaton za a yi cikin kankanin lokaci, sai ga shi sun yi sa’o’i babu biyan bukata.
“Wahalar da muke sha ta wuce misali, wahala muka sha kafin mu samu wannan kudin, amma kuma a ce sai mun wahala kafin mu taba kudinmu.”
“Shafin nasu ba ya aiki kuma babu wanda ya kawo mana fom mu cike.
“Wasunmu dage Suleja suka zo suna zaton za su ajiye tsoffin kudadensu su koma gida, amma tsugune ba ta kare ba. Sai ka wahala kafin ka ajiye tsoffin kudinka, sai ka wahala ka samu sabbi.”
Hakan ne ya fusata su, suka tare kofar shiga bankin na tsawon awanni.