Kungiyar Mamallakan Motocin Haya ta Najeriya (NARTO) ta janye yajin aikin tireloli da tankokin man fetur da ta fara gudanarwa.
Bayan masu ruwa da tsaki sun sa baki, NARTO ta umarci direbobin da su ci gaba da aiki saboda Gwamnati Tarayya ta janye kudirinta na hana
tankoki masu lodin lita 45,000 dauka mai a Najeriya.
Shugaban kungiyar ta kasa, Alhaji Yusuf Othman, ya ce “Sakamakon sa baki da Shugaban Kamfanin Mai na kasa (NNPC), Mele Kyari da Shugaban Hukumar tsaro ta DSS, muna kira ga duk mambobinmu na kasa su koma aiki.
“Wannan umarni ne na janye yajin aikin har sai Janairun 2021 domin samun damar yin shawarwari.
- ‘Manyan motoci na barazana ga rayukanmu’
- Tsadar kaya ta tilasta rufe ‘Gidan abincin N30
- Kwanan nan za a dawo da aikin Umarah —Saudiyya
“Muna godiya da goyon bayan da dukkannin mambobinmu suka ba mu da hakurin da suka yi na gani cewar an gudanar da sulhu kan matsalar”.
- Matsalar da ke tafe
Sai dai ya ce muddin gwamnati ta hana tankokin masu daukar lita 45,000 yin lodi, to hakan zai haifar da matsalolin rashin aikin yi ga direbobi da yaran mota da masu gyaran manyan motoci
akalla 40,000.
“Gaskiya har yanzu mun kasa fahimtar abin da zai sa gwamnati ta dauki
wannan matakin.
“Muna kuma kira ga gwamnati ta tausaya wa halin da
mambobinmu suke ciki, musamman a radadin tattalin arziki da ake
fuskanta.
“A bamu isashen lokaci domin ganin mun tara kudaden za mu
sauya fasalin tankokinmu da yanayi jigilar”, inji shi.
- Shirin shiga yajin aiki
A baya kungiyar ta umarci ‘ya’yanta da su tsayar da jigilar man fetur da sauran ayyukansu a ranaku Talata da Laraba saboda hana tankokin aiki.
Ta kuma sanar da Gwamnatin Tarayya cewar za su shiga yajin aikin
kwanaki 10 daga ranar Alhamis 24 ga watan Satumba, 2020.
Hakan ya sa Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) Mele Kyari da
Shugaban Hukumar tsaro ta DSS suka lallashi kungiyar ta amince
da dage yajin aikin zuwa ranar 1 ga watan Janairu 2021.
Usman ya ce sun dage ranar ne domin bayar da damar tattaunawa
da masu ruwa da tsaki a harkar.