✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu kwacen waya sun kashe matashi a Kano

Babu shakka kwacen wayoyin hannu ya zama ruwan dare a birnin Dabo.

Wasu masu ta’adar yi wa mutane kwacen waya sun kashe wani matashi mai suna Umar Muhammad Ahmad a Jihar Kano.

Wani dan uwan mamacin da aka daba wa wuka, Mustapha Modi Adamu ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa kan shafinsa na Facebook a ranar Lahadi.

A cewarsa, a daren ranar Asabar ne masu kwacen wayar suka tare mamacin a karkashin gadar sama da ake gina wa a Kasuwar Kantin Kwari, inda suka daba masa wuka kuma suka yi awon gaba da wayarsa ta hannu.

Babu shakka lamari na ta’adar kwacen wayoyin hannu ya zama ruwan dare a birnin Dabo, duba da yadda ya zama abun fargaba ga mazauna jihar duk da kokarin da gwamnati da jami’an tsaro ke yi don ganin sun kawo karshe lamarin.

Rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun fuskanci wannan mummunar barazana ta masu kwacen yawa, inda aka samu dimbin jama’a da suka rasa rayukansu yayin da kuma wasu suka samu rauni iri daban-daban.

Tun watannin baya dai gwamnatin Jihar ta sanar da dasa na’urorin daukar hoton bidiyo na CCTV, a wurare daban-daban a fadin jihar a yunkurinta na sanya idanu da zummar magance ire-iren wadannan matsaloli.

Yunkurin tabbatar da ingancin wannan rahoto daga bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sanda Jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ci tura.