✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu kwacen mota 3 sun shiga hannu a Abuja

Kwamishinan ya ce ana ci gaba da bincike a kan su don samun bayanai.

Rundunar ’yan sanda ta kama wasu mutum uku da ake zargin su da fashi da makami da kuma kwacen motoci a Abuja.

Kwamishinan ’yan sandan Abuja, Garba Haruna, yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar ’yan sandan ya ce an kama su ne bayan wani dauki-ba-dadi da jami’an rundunar.

Ya ce mutanen ukun na da alaka da yawaitar fashi da makami da kwacen mota Abuja.

“An kama su da motoci biyu; Toyota Corolla mai launin toka mara lamba da bakar Toyota Camry 206, ita ma ba ta da lamba, da kuma bindiga guda daya,” in ji shi.

Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike don gano ragowar da suke aikata laifukan.

Ya kuma tabbatar wa mazauna Abuja cewa, rundunar ’yan sandan na ci gaba da jajircewa wajen samar da tsaro da kwanciyar hankali.

Kazalika, ya bukaci mazauna Abuja da su kasance cikin shiri da bayar da rahoton gaggawa ga ’yan sanda ta wadannan lambobi domin kai musu dauki 08032003913, 08061581938, 07057337658.38.