✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu kudin Najeriya na da hannu dumu-dumu a matsalar tsaro – Al-Mustapha

Ya ce yaki da ayyukan ta’addanci a Najeriya na bukatar hada karfi da karfe.

Tsohon Babban Dogarin marigayi Shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha, wato Manjo Hamza Al-Mustapha, ya ce masu kudin da suke safarar makamai da miyagun kwayoyi ne ummul-aba’isun matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.

A cewarsa, yaki da ayyukan ta’addanci a Najeriya na bukatar hada karfi da karfe na kowa daga dukkan jama’a wajen kawo karshen matsalar.

Manjo Al-Mustapha ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da Sashen Hausa na Muryar Amurka.

Ya ce, “Lokaci ya yi da duk wani dan Najeriya da ke da kishin kasar da ma nahiyar Afirka zai tashi ya bayar da tasa gudunmawar. Abubuwa ba sa tafiya yadda ya kamata.

“Mutane na kashe kudadensu wajen rura wutar rikici, kuma alamu na nuni da cewa suna cin nasara.

“La’akari da yadda suke samun makamai yau a Afirka, da ma miyagun kwayoyi da dama daga mutanen da suke samar musu da su, alamu sun nuna cewa sun fara nuna sun fi karfin dokokinmu na Afirka, musamman ma na Najeriya,” inji shi.

Manjo Al-Mustapha ya kuma koka kan cewa wasu ’yan tsirarun mutane ne ke cin gajiyar albarkatun ma’adinai a Najeriya, kuma bisa ga dukkan alamu, sun fi karfin kowa.