✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu Keke Napep sun shiga yajin aiki a Maiduguri

Masu jigilar fasinjoji a babur mai kafa uku wanda aka fi sani da Keke Napep, sun shiga yajin aiki a birnin Maiduguri saboda cin zarafi…

Masu jigilar fasinjoji a babur mai kafa uku wanda aka fi sani da Keke Napep, sun shiga yajin aiki a birnin Maiduguri saboda cin zarafi da suka ce suna fuskanta daga wurin mahukunta.

Hakan ya sanya fasinjoji da dama sun rasa madafa ta yin sabgoginsu cikin sukuni, inda hatta dalibai sai sun yi doguwar tafiya kafin su isa makarantunsu.

Wani direba mai suna Usman Modu, ya bayyana yadda ake cin zarafinsu da sunan haraji, “Idan ka biya haraji a kurarren lokaci sai ka biya tara ko su kwace maka makullin babur.

“Sannan suna ci mana zarafi game da shigar kaya, misali idan ka sa riga mara hannu, to ba za ka yi aiki ba wannan ranar ba.

“Masu karbar harajin na tambayar mutane takardar shaidar tuki, wanda ba ya daga cikin ka’idodinsu,” a cewar Modu.

Wakilin Aminiya ya yi kokarin jin ta bakin masu ruwa da tsaki kan karbar haraji a Jihar Borno game da takaddamar sai dai lamarin ya ci tura.

Wata mai mata mai sana’ar sayar da abinci, Amina Saleh, da ke kan titin kasuwar Baga, ta ce da yawa daga cikin masu cin abinci a wajen da safe ba su kawo mata ziyara ba saboda yajin aikin da masu baburan suka shiga.

Kazalika, wata daliba da ke rukunin gidaje na Ibrahim Taiwo a Maiduguri, ta bayyana yadda ta yi doguwar tafiya a kafa kafin ta isa makaranta sakamakon rashin abin hawa.