✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu Gurasa sun yi zanga-zanga kan tsadar fulawa a Kano

Masu gurasar sun koka kan yadda tsadar fulawar ta shafi kasuwancinsu.

Masu sana’ar Gurasa a Jihar Kano, sun gudanar da zanga-zangar lumana don nuna rashin jin dadinsu kan yadda fulawa ta yi tsada a jihar.

A cewar Shugabar Kungiyar Masu Sana’ar Gurasa, Fatima Auwal Chediyar ‘Yan Gurasa, ta ce sun shiga yajin aiki har sai farashin fulawa ya daidaita a jihar.

“Farashin fulawa wadda ita ce kashin bayan sana’armu ta yi tsada, kullum idan muka je saya farashi na karuwa, farashin buhun a yanzu ya kai Naira 40,000, me za mu yi?”

Ta bayyana cewa, galibin masu sana’ar mata ne marasa aure da ke daukar nauyin iyalansu, inda ta ce hakan na barazana ga rayuwarsu.

“A baya muna karbar fulawa a kan bashi, muna biya bayan mun sayar amma a yanzu hakan ba ya samuwa.

“Dalilin wannan zanga-zangar ta lumana ita ce, jawo hankalin hukumomi cewa muna fuskantar babbar matsala, nan gaba kadan ba za mu iya kasuwanci ba idan ba a yi wani abu a kai ba.”

Ta kuma jaddada cewa ba su da wani zabi da ya wuce su daina kasuwancin su zubawa sarautar Ubangiji ido.

“Yawancin mutane masu karamin karfi suna amfani da gurasa a maimakon burodi don haka ba mu kadai hakan za ta shafa ba, har da talakawa da suka dogara da mu.”