✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu gine-gine a filayen Gwamnatin Kano su dakata —Abba Gida-Gida

Mun kudiri aniyar dawo da tsarin birnin Kano.

Zababben Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya shawarci duk wasu masu gine-gine a filayen gwamnatin jihar da su dakata nan take.

Wannan sanarwa na kunshe ne cikin wani sako da zababben gwamnan ya wallafa safiyar Juma’a a shafinsa na Facebook.

A cewarsa, “kamar yadda muka kudiri aniyar dawo da tsarin birnin Kano, ina shawartar jama’a da su daina duk wani aikin gine-gine a filayen gwamnati, a ciki da wajen makarantu.

“Wuraren addini da na al’adu, da dukkan asibitoci, da makarbarta, da kume gefen katangar birnin Jihar Kano [ganuwa].”

Haka kuma, a kunshin sanarwar da mai magana da yawun zababben gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar, an kuma shawarci dakatar da rushewa ko kuma ci gaba da aikin duk wasu gine-gine a filayen gwamnatin jihar.