A ranar Talatar da ta gabata ce Shugabanin Kungiyar Mansu Gidajen Man fetur suka yi zanga-zangar lumana a Kamfanin Man Fetur ta Kasa (KRPC) na Kamfanin NNPC da ke Kaduna saboda nuna rashin jin dadinsu kan yadda ba a bin ka’ida wajen jigilar mai a kamfanin. Sun nuna cewa a kan nuna son kai tare da yin alfama wajen yin jigilar man fetur a kamfanin wanda hakan ke sa ake danne hakkin wadansu daga cikin mambobinsu. Shugaban kungiyar, Kwamared Abdulfatahi Murtala wanda shi ne ya jagoranci sauran ’yan kungiyar zuwa bangaren KRPC a Kaduna ya ce ba za su yarda a rika nuna son kai da kin bin dokoki wajen yin jigilar man fetur ba a kamfanin.
“Dalilin zuwanmu nan shi ne domin nuna kin amincewa da zalunci da ake neman yi a wannan kamfani na matatar mai da ke Kaduna. Ba za mu yarda da zalunce mu ba. An ce babu man fetur amma kuma an aiko da takarda daga Abuja cewa a bai wa wani mutum motoci takwas, ke nan akwai mai a ajiye.
Ba mu ce kada a yi alfarma ba, amma akwai motoci kusan bakwai da suka dade suna jiran a ba su mai amma ba a ba su ba, kimanin wata biyu ke nan suna jira. Kuma sun biya kudinsu amma har yanzu ba a ba su kaya ba. Don haka muke nuna rashin jin dadinmu,” inji shi.
Ya mika godiyarsa ga sauran ’ya’yan kungiyar kamar Kungiyar Direbobin Tanka (PTD) da sauransu bisa goyon baya da suka ba su na hana a yi jigilar mai a kamfanin.
A jawabin shugaban yanki na NUPENG, Kwamared Ahmed Tijjani ya bayyana goyon bayansa ga wannan zanga-zanga da masu gidajen man fetur suka yi inda ya ce a shirye suke su tabbatar da an tsayar da adalci a kamfanin.
“Za mu tattauna da duk wanda abin ya shafa don ganin a tsayar da adalci, babu adalci a ce mutum ya biya kudinsa na tsawon lokaci amma a hana shi kaya. Don haka za mu bincika mu ga su wane ne suka aiko da takardar idan ya kama mu gana da Janar Manajan NNPC za mu nemi yin hakan don a magance matsalar,” inji shi.