Kungiyar masu gidajen burodi ta kasa reshen jihar Kogi ta ce daga ranar Laraba za ta fara yajin aiki saboda tsadar fulawa da sauran kayan hada burodin.
Shugaban kungiyar reshen jihar, Cif Gabriel Adeniyi, ne ya bayyana haka a Lokoja babban birnin jihar, inda ya ce za su bi sahun uwar kungiyar ta kasa a yajin aiakin da ta shirua farwa daga ranar 20 ga watan Yulin 2022.
Ya ce babu makawa za su tsunduma yajin aikin ya zama wajibi saboda halin da masu sana’ar ke ciki a Najeriya, kuma gwamnati ta ki ta kawo musu dauki duk da koke-koken da suka jima suna yi.
Cif Gabriel ya ce daga cikin dalilan da suka sa za su dauki matakin akwai akwai tsadar kayayyaki, yawan haraji, karancin kayan yin burodin da sauransu.
Shugaban ya kuma ce, “Tun lokacin da aka hana shigo da fulawa cikin kasa, babu wani yunkuri da aka yi wajen bunkasa noman alkama kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta yi, ta bakin Ma’aikatar Gona.”
Ya kuma ce tsawon lokaci gwamnati ta ki amincewa ta ba su tallafin da ta alkawarta na bayar da basussuka marasa ruwa.
“Da zarar mun fara yajin aikin, ba za a rika ganin kayayyakinmu ba a kasuwanni da shaguna da wuraren sayar da abinci, don tilasta wa gwamnati yin abin da ya dace.
“Yawan tashin farashin kayayyakin yin burodi, musamman fulawa da sukari, wadanda suka ta’azzara tashin farashin tare da tilasta wa wasu rufe wurarensu,” inji shi.
Daga nan sai shugaban ya roki gwamnati da ta kawo agajin gaggawa don kaucewa jefa miliyoyin masu cin abinci a harkar rasa ayyukansu.