✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kwamishinan Neja ya sa masu garkuwa da shi zubar da hawaye

’Yan bindigar da kansu suka kira iyalansa su je su dauke shi.

Masu garkuwa da suka sace Kwamishinan Yada Labaran Jihar Neja, Muhammad Sani Idris sun sako shi bayan ya fada musu abin da ya sa zu zubar da hawaye.

Kwamishinan, wanda aka yi garkuwa da shi a safiyar ranar Litinin a gidansa da ke unguwar Babban-Tunga da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna ya koma gida ranar Alhamis da dare.

Iyalansa sun tabbatar wa wakilinmu cewa a cikin daren ne masu garkuwar da kansu suka kira su a waya suka kwatanta musu wurin da za su je su dauke shi, kuma suka je wurin suka dauko shi.

“Abin da muka lura shi ne an dauko masu garkuwar ne daga Jihar Zamfara don su yi garkuwa da shi Kwaminan na Jihar Neja, aka ce musu wai ana biyan shi kusan Naira miliyan 200 a duk wata.

“Abin da aka so su yi shi ne su karbi kudin fansa daga baya sai su kashe shi.

“Amma ya yi nasarar fahimtar da su, suka gane gaskiyar abin da ake biyan shi, wanda hakan ya sa su zubar da hawaye, har suka yi nadamar abin da suka aikata.”

Idan ba a manta ba, da fakro masu garkuwar sun bukaci Naira miliyan 500 a matsayin kudin fansar Kwamishinan, amma daga baya suka rage zuwa Naira miliyan 70 a ranar Laraba da dare, kafin daga baya su sako shi ranar Alhamis da dare.