✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa sun sako hadimin gwamnan Nasarawa

An sako mataimaki na musamman ga gwamnan Nasarawa a kan al’amuran kananan hukumomi da masarautu, John Mamman, wanda masu garkuwa da mutane ke rike da…

An sako mataimaki na musamman ga gwamnan Nasarawa a kan al’amuran kananan hukumomi da masarautu, John Mamman, wanda masu garkuwa da mutane ke rike da shi.

Wani makusancinsa da ya bukaci a sakaya sunanshi ya bayyana wa Aminiya cewa an sako Mista Mamman ne a daren Talata.

Masu garkuwa da mutanen sun shiga gidan jami’in da ke unguwar Dari a karamar hukumar Kokona da yammacin ranar Asabar bayan sun yi ta harbi a iska sannan suka yi awon gaba da shi.

Wasu daga cikin mazauna unguwar ta Dari sun yi nasarar kama mutum guda da ake zargin yana cikin masu garkuwar kuma an mika shi ga ‘yan sanda.

Rahotanni sun nuna cewa tun da farko dai masu garkuwar sun bukaci a biya kudin fansa Naira miliyan 150, amma daga bisani suka amince a biya su Naira miliyan 20 da yammacin ranar Litinin.

Sai dai rahoton bai tabbatar da ko an biya kudin fansar ba kafin a sako Mista Mamman.

Kakakin rundunar ’yan sanda ta jihar Nasarawa, ASP Ramhan Nansel, ya tabbatar da sakin John Mamman.