✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan bindiga suka sako Daliban Islamiyyar Tegina

An sako daliban bayan sun kwana 88 a hannun masu garkuwa.

’Yan bindiga sun sako ragowar daliban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko Salihu da ke garin Tegina na Jihar Neja, bayan yaran sun shafe kwana 88 a hannunsu.

Hukumar makarantar da iyayen daliban da wasu majiyoyi a garin Tegina sun tabbatar wa Aminiya cewa an sako ragowar yaran ne da dare, ranar Alhamis 26 ga Agusta, 2021.

Da yake tabbatar mana ta waya cewa an sako ’ya’yan nasu, daya daga cikin iyayen daliban ya yi godiya ga Allah da cewa, “’Ya’yanmu sun dawo; Yanzu maganar nan da nake muku suna hanya za a kai su Gidan Gwamnati da ke Minna”.

Shugaban Makarantar ta Salihu Tanko, Alhaji Garba Alhassan, ya tabbatar mana cewa masu garkuwar sun saki yaran ne a kusa da wani kauye da ke yankin Birnin-Gwari a Jihar Kaduna.

A lokacin da muka zanta da shi ya tabbatar mana cewa daliban suna hanyarsu ta zuwa Minna, babban birnin Jihar Neja, inda jami’an gwamnati za su karbe su sannan a duba lafiyarsu.

Wasu daga cikin Daliban Tegina da aka sako.

Rahotanni sun nuna cewa an sako ragowar daliban na Tegina ne bayan an biya kudin fansarsu Naira miliyan 18 da kuma babura da ’yan bindiga suka bukata.

Bayanan sun nuna cewa wasu manyan ’yan siyasa ne a Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja suka taimaka da kudaden.

Fadi-tashin ceto Daliban Tegina

A ranar 30 ga watan Mayu, 2021 ne ’yan bindiga suka kutsa cikin Makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko da ke garin na Tegina suka yi awon gaba da dalibai 136.

Sace daliban na Tegina ya sanya girgiza mutane matuka, sannan daga baya masu garkuwar suka bukaci kudin fansa Naira miliyan 200 a kan kananan yaran.

Lamarin ya kai ga matakin da aka zuba wa Sarautar Allah ido saboda masu garkuwar sun ki su sako yaran, bayan sun karbi Naira miliya 50 da iyayen daliban da sauran al’umma suka yi karo-karo domin ganin an sako su.

Idan ba a manta ba, mun kawo rahoto cewa 17 daga cikin daliban na Tegina da aka yi garkuwa da su, sun kubuta daga hannun ’yan bindigar, wasu shida kuma sun rasu a hannun miyagun.

Daliban Tegina

Daga bisani masu garkuwar suka amince su sako ragowar daliban 116 da ke hannunsu, suka kuma rage kudin fansar da suka nema na Naira miliyan 200 zuwa miliyan 50.

Bayan Naira miliyan 20 da aka ba wa masu garkuwar a watan Yuni, a baya-bayan nan an kara yin karo-karo aka tara Naira miliyan 30 da aka shirya aka kuma kai musu a wani daji.

Da aka kai musu sai suka yi ikirarin cewa kudin bai cika ba da Naira miliyan 4.6, saboda haka suka karbe kudin, suka rike dan aiken sannan suka ci gaba da garkuwa da yaran.

Daga baya suka kira waya suna neman a kawo cikon Naira miliyan 4.6  din, da wani Naira miliyan biyu a matsayin cikon Naira miliyan 20 da aka kai musu da farko ne da bai cika ba —Jumulla Naira miliyan 6.6 ke nan.

Bayan haka kuma za a kara musu da sabbin babura kirar Bajaj kafin su sako wadanda ke hannun nasu.

Sagir Kano Saleh da Fidelis Mac-Leva da Abubakar Akote (Minna)