‘Yan bindigar da suka yi garkuwa suke kuma ci gaba da rike da jami’an ‘yan sanda shida masu mukamin ASP na kusan tsawon mako daya na neman Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansarsu.
Rahotanni sun nuna ‘yan sandan na daga cikin guda taran da aka sace jim kadan da kara musu matsayi zuwa matakin ASP, kuma suna aiki ne da rundunar a jihar Borno.
- An ceto mutum 9 da aka yi garkuwa da su a hanyar Abuja
- Na ga wulakanci a Gwamnatin Buhari —Zainab Buba Galadima
Suna dai kan hanyarsu ne daga Bornon zuwa Zamfara saboda sauyin wurin aikin da aka yi musu lokacin da aka yi musu kwanton-bauna a Dogon-Daji na jihar Katsina sannan aka gudu da su cikin daji.
Wata majiya ta ce su taran na tsaka da shirin tafiya Zamfaran ne daya daga cikinsu ya canza shawara ya tafi a motar haya.
Ya ce, “Da zuwansu Kano sai direban ya ce su canza mota, tasa ta lalace.
“Da suka kama hanyar zuwa Zamfara daga Maiduguri sai daya daga cikinsu ya canza shawara ba zai bi ayarinsu ba. Ya ce yana da uzurin da zai yi, zai same su daga baya.
Ko da suka je Dogon Daji a jihar Katsina sai ‘yan bindiga suka yi awon gaba da su. An tafi da shida daga cikinsu, biyu kuma suk tsere, yayin da aka harbi wani a kafa ko da dai bai mutu ba.
“Ragowar guda shidan da aka sace kuma yanzu ana neman N100m daga wajensu,” inji shi.
Bincike ya nuna tuni iyalan ‘yan sandan suka fara fadi-tashin nemowa ‘yan uwan nasu mafita bayan neman kudin fansar da ‘yan bindigar suka yi.
Rahotanni na nuna cewa iyalan na kokarin harhada N500,000 kowannensu.
Kakakin rundunar na kasa, DCP Frank Mba ya ki ya ce uffan kan lamarin saboda bai amsa kira waya da sakon kar-ta-kwanan da aka tura masa ba ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.