✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa da Shugaban APC sun riƙe masu kai kuɗin fansa

Maharan sun far masa suka fito da shi daga cikin motarsu, sa’annan suka make shi da gungumen ice, suka tafi da shi.

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da Shugaban Jami’iyyar APC a Ƙaramar Hukumar Ose a Jihar Ondo, Nelson Adepoyigi, sun riƙe mutanen da suka kai musu kuɗin fansarsa, sa’annan suka ƙara ƙudin fansar da suka nema da ninki shiga.

A ranar Litinin da dare ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da Honorabul Nelson Adepoyigi a ƙofar gidansa inda suka nemi kuɗin fansa naira miliyan 100 kafin daga bisani a daidaita a kan miliyan biyar.

Majiyoyin sun a lokacin da yake ƙoƙarin shiga gida ne maharan suka far masa suka fito da shi daga cikin motarsu, sa’annan suka make shi da gungumen ice sa’annan suka tafi da shi.

Wani makusanci ga waɗanda suka kai kuɗin ya bayyana cewa, “Bayan daidaitawa da ’yan bindigar a kan kuɗin fansa, da masu biyan kuɗin suka kai sai ’yan bindigar suka kama su suka ɗaure a cikin dajin.”

Da yake tabbatar da faruwar abin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Ose, Kolapo Ojo, ya ce yanzu ’yan bindigar sun ƙara yawan kuɗin fansar zuwa Naira miliyan 30 kafin sakin ɗan siyasan da sauran mutanen biyu.

Sai dai ya buƙaci jama’a su kwantar da hankalinsu, jami’an tsaro na yin duk mai yiwuwa domin kuɓutar da duk mutanen.

Kakakin ’yan sanda a jihar, Olusola Olayinka, ya shaida wa Aminiya cewa rundunar ta haɗa guiwa da jami’an tsaron sa kai da maharba domin zaƙulo ’yan bindigar.