Masu garkuwa da Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu, da ke Karamar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna sun bukaci a ba su Naira miliyan 200 a matsayin kudin fansa.
An dai yi garkuwa da sarkin ne da wasu iyalansa su 12 a fadarsa da ke garin na Kajuru a da sanyin safiyar ranar Lahadi.
- Za a daure ta shekara 5 saboda kai wa saurayinta kwaya gidan yari
- Kyaftin din Super Eagles, Ahmed Musa ya kara aure
Daya daga cikin masu rike da sarauta a masarautar ne ya tabbatarwa da Aminiya cewa masu garkuwar sun tuntube su ta waya suna neman a basu N200m.
Muna tafe da karin bayani….