✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindigar da suka sace ’yan gida daya na neman miliyan N500

’Yan bindigar na neman miliyan N100 kan kowane mutum daya cikin iyalen wani tela

’Yan bindigar da suka sace wata uwa da ’ya’yanta hudu a unguwar Barakallahu ta Jihar Kaduna na neman Naira miliyan 500 a matsayin kudin fansa.

A daren Juma’ar da ta gabata ce masu garkuwar suka yi wa unguwar dirar mikiya inda suka sace matar wani tela mai suna Abdulsalam Haruna da ’ya’yanta hudu, kamar yadda ya shaida wa Aminiya.

“Sun tuntube ni a waya ranar Lahadi kan cewa na biya Naira miliyan 100 a kan kowane mutum daya, jimlar Naira miliyan 500 ke nan.

“Fisabilillahi ina zan ga wannan kudin a matsayina na tela?

“Muna nan dai muna ci gaba da tattaunawa da su domin ganin sun yi sassauci saboda gaskiya yanzu ni ba ni da wani abin da zan iya ba su. Allah dai Ya kawo min dauki”, inji Malam Abdussalam.

Ya ce wadanda aka sace din sun hada d Mustapha Abdulsalam, Hauwa Abdulsalam, Muhammad Abdulsalam, Ummul-Khairi Abdulsalam, sai kuma mahaifiyarsu, Hajara Abdulsalam.

Daga nan sai ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da Ma’aikatar Tsaro da Al’amuran Cikin Gida dsa su kawo masa dauki.

Sai dai ya zuwa yanzu, rundunar ’yan sandan jihar ba ta ce uffan kan lamarin ba.