‘Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sako shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, wato CAN, reshen jihar Nasarawa, Bishop Joseph Masin.
Wasu masu dauke da makamai ne dai suka yi dirar mikiya cikin daren 27 ga watan Mayu a gidansa da ke Bukan Sidi a birnin Lafia suka yi awon gaba da shi.
Daya daga cikin ‘ya’yansa, Pastor Sam Joseph yace “An sako Bishop din da misalin karfe 11 na daren Asabar kuma ya dawo gida misalin karfe 2 na dare.
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban CAN a Nasarawa
- An yi garkuwa da mataimakin shugaban APC na Kaduna
Ya zuwa yanzu dai ba a san ko an biya wasu kudade saboda a sako shi ba.
Wata majiya ta bayyana cewa masu garkuwa da shi din sun bukaci a ba su Naira miliyan 20 kwana daya bayan sace shi.
Tsohon sakataren kungiyar, Yohanna Samari, ya ce masu garkuwar sun dauki malamin addinin ne a kan babur lokacin da suka sace shi.