Wadanda suka yi garkuwa da ’yar shekara 11 nan mai suna Nana Usman, ’yar wani dan kasuwa mai suna Mansur Abubakar da ke zaune a garin Malumfashi a Jihar Katsina sun nemi a basu Naira miliyan 100 kafin su saki yarinyar.
Wani da ke kusa da iyalan mutumin ya shaida wa Aminiya cewa wadanda suka yi garkuwa da yarinyar sun kira mutumin har sau uku suna neman a basu kudin kafin su sake ta.
Majiyar ta ce mahaifin yarinyar ya damu kwarai da gaske saboda tsoro ma ya bar yankin ya koma wani wurin da ba a sani ba.
An sace Nana da misalin karfe 11 da rabi na dare a karshen makon da ya gabata yayin da ’yan bindiga kimanin ishirin da ke kan babura da motoci suka yi wa gidansu dirar mikiya.
Mazauna unguwar da dan kasuwar yake zaune sun shiga tashin hankali da fargaba tun lokacin lamarin ya auku.
Wani rahoto da ba a tabbatar ba ya nuna cewa biyu daga cikin ’yan bindigar sun ji munanan ranuka yayin wata musayar wuta da wani dan sanda, kuma tuni har ’yan sanda sun kama daya daga cikinsu.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin rundunar ’yan sandan ya ci tura.