Wasu masu garkuwa da mutane a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari sun kashe wani Bakano dan kasuwa bayan karbar kudin fansa daga iyalansa.
Mutumin, mai suna Umar Sani, wanda aka fi sani da Magaji, ya hadu da iftila’in ne bayan maharan sun sace shi a kan hanyarsa ta zuwa garin Buruku tare da wasu ’yan uwansa ’yan kasuwa da nufin saya mangwaro.
- Shin matasa na koyon dabanci a fina-finan Hausa?
- Ranar littafi ta duniya: ‘Har a nade kasa ba za a daina karanta littafi ba’
Sai dai daga bisani mutanen da aka sace su tare wadanda a yanzu haka suka kubuta bayan biya musu kudin fansa, sun tabbatar da cewa Magajin ya rasu a hannun ’yan bindigar.
Mamacin dai dan asalin unguwar Fagge ne da ke birnin Kano, wanda yanzu yake zaune tare da iyalansa a garin Bichi na Jihar ta Kano.
Wani yaya ga mamacin mai suna Hussaini Sani, wanda ya tabbatar wa Aminiya labarin kisan, ya kuma ce maharan sun yi yunkurin karbar wata Naira miliyan 20 daga hannunsu, duk da cewa sun kashe shi.
Hussaini ya ce, “Su tara aka sace kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, a kan hanyarsu ta zuwa Buruku sayo mangwaro. Amma daga bisani sun saki uku daga cikinsu.
“Bayan wani lokaci an yi ciniki inda suka amince za su saki duka mutum shidan bayan biyan kudin fansa, amma kawai sai suka saki mutum biyar, ban da dan uwan namu.
“Da muka tambayi mutanen da suka dawo, sai suka tabbatar mana da cewa masu garkuwar da su sun kashe shi.
“Sai muka kira masu garkuwar da lambar da muka yi ciniki da su, amma suka ce mana wai har yanzu yana da rai, suna so mu kara basu wasu kudaden.
“Amma da muka tsaya kai da fata sai mun ji muryarsa tukunna, sai daga karshe suka tabbatar mana da cewa sun kashe shi,” inji Hussaini.
Shi kuwa Alhaji Ashiru Fagge, wanda shi ne babban yaya ga mamacin, ya ce masu garkuwar sun so su yaudare su cewa dan uwan nasu na raye, inda suka nemi a sake biyansu Naira miliyan 20.
Ya ce, “Mun kira su ranar Alhamis don su hada mu da dan uwanmu indai yana raye kafin mu ci gaba da wani ciniki.
“Sun yi alkawari a lokacin cewa za su kira mu wajen misalin karfe 6:30 na yamma, amma wayar tasu na kashe. Har sai kashegarin Juma’a sannan da muka matsa suka tabbatar mana da cewa sun kashe shi.
“Da muka tambaye su gawar, sai suka ce ai tuni an binne shi a dajin,” inji Alhaji Ashiru.
Sai dai ya ki ya fadi ko nawa suka biya masu garkuwar kudin fansa, saboda ya ce hadawa aka yi aka biya wa mutum shidan gaba daya, don haka bai san nawa aka kai musu ba.
Kisan Magajin dai na zuwa ne kasa da kwana 10 bayan an gano gawar wani Bakanon dan kasuwar bayan karbar kudin fansarsa, shi ma dai a yankin na Birnin Gwari.