✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa da mutane sun hana Katsinawa sakat

Jihar Katsina wadda ake yi wa kallon jihar da ke da zaman lafiya da tsaro, a yanzu tana bisa hanyar komawa kasuwar masu garkuwa da…

Jihar Katsina wadda ake yi wa kallon jihar da ke da zaman lafiya da tsaro, a yanzu tana bisa hanyar komawa kasuwar masu garkuwa da mutane.

A ’yan shekarun baya, jihar ta yi fama da matsalar barayin shanu bayan arangama a tsakanin manoma da makiyaya Fulani. Wannan matsala ta satar shanu ta yi ƙamari a tsakanin kananan hukumomin Jibiya da ke da iyaka da Jamhuriyar Nijar da kuma Jihar Zamfara. Sauran ƙananan hukumomin sun haɗa da Batsari wadda Dajin Rugu ke cikinta, bayan iyakar da ta yi da jihar ta Zamfara. Akwai Safana da Ɗanmusa da Kanƙara da Faskari da Dandume da Sabuwa, waɗanda suke da iyaka da Dajin Birnin Gwari da ke  Jihar Kaduna.

Zuwan Gwamna Aminu Bello Masari a jihar ya yi ƙoƙarin kafa kwamitin sasanci da yafiya ga Fulanin da suka yi watsi da waccan ɓarna da asarar rayuka da dukiyoyi, kwamitin da ya yi nasarar tsayar da waccan matsala da aka yi wa laƙabi da “Kiwo Haram.” Wancan sasanci ya sake maido da zaman lafiya a waɗannan ƙananan hukumomi da maƙwabtansu, waɗanda har sun fara karɓar baƙuncin ’yan gudun hijra.

Bayan samar da zaman lafiyar da Gwamna Masari ya yi ƙoƙarin yi, sai ga shi jihar ta sake faɗawa cikin matsalar masu garkuwa da mutane, abin da ke neman zama ruwan dare. Yunkuri na baya-bayan nan shi ne wanda aka yi a Karamar Hukumar Faskari, inda wadansu masu garkuwa da mutane suka zagaye gidan Alhaji Nasiru Bala a ƙauyen Kamfanin Daudawa. Masu garkuwar ba su samu nasarar tafiya da shi ba kamar yadda majiyar ’yan sanda a jihar ta ce. Hakan ya faru ne saboda ɗaukin da aka kai wanda ya sa har suka kama ɗaya da cikinsu, yayin da sauran suka tsere.

Kazalika, rundunar ta gabatar da wadansu da ta kama a ƙoƙarin da suke yi na daƙile waɗannan miyagun mutane. Ɗaya daga cikinsu ya ce babban aikinsa shi ne, in an kamo an kawo shi ke tsarewa. “Ana ba ni Naira dubu 20 duk lokacin da aka yi biya,” inji wannan maigadi, wanda ya ce ya fito daga Dajin Birnin Gwari ne. A yanzu kuma yana nan cikin Dajin Rugu a ƙarƙashin jagorancin Ruga Kacalla. Ya ce ya taɓa zama a ƙarƙashin Buharin Daji, yana yi masa kiwo a ba shi saniya ɗaya duk shekara. Bayan mutuwar Buharin ne ya dawo wannan fage na barayi.

An dai fara samun labarin sacewa da yin garkuwa da mutane a ’yan watannin baya a kan hanyar zuwa Birnin Gwari ta Jihar Kaduna, a cikin dajin da ya haɗa kananan hukumomin Dandume da Sabuwa, inda masu garkuwar suka yi awon gaba da wadansu mutane shida da aka ce dukansu ’yan garin Karofi ne a hanyarsu ta dawowa gida daga Legas.

Har ila yau, duk a batun sacewa da garkuwa da waɗanda aka sace a kan iyakokin da ke kusa da dazuzzukan Birnin Gwari da Dajin Rugu, hanyoyi biyu ne ake amfani da su a wajen satar, kamar yadda Aminiya ta gano a binciken da ta yi. Hanya ta farko ita ce ta yin amfani da ciki ko bakin iyaka da waɗannan dazuzzuka, sai hanya ta biyu ta yin amfani da sinadarin ɓatar da hankali.

A irin waccan hanya ta amfani da bakin dajin ce aka yi amfani da ita wajen ɗauke kansiloli biyu na Safana a hanyarsu ta zuwa Batsari. An dai biya kudin fansa Naira milyan hudu maimakon miliyan 50 kafin su dawo ga iyalansu bayan sun kwashe kwana 26 a hannun masu garkuwar.

Duk da cewa Karamar Hukumar Dutsin-ma ba ta raɓe da kowane daji daga cikin waɗancan da aka ambata, amma ta zamo tamkar a cikinta ne waɗancan barayi ke cin kasuwa. A tsakanin watan Nuwanba zuwa Disamban bana, satar mutanen ta zama ruwan dare a karamar hukumar. Daga cikin mutanen da aka sace akwai Ibrahim Musa Jabi Manajan Gidan Man Shema, wanda barayin suka sace shi da dare a gidansa da ke bakin kasuwa a titin zuwa Tsaskiya. Sai Zainab Musa wadda take ma’aikaciya a Babban Asibitin Dutsin-ma.

An dauke Zainab a kauyen Maitsanni, shi ma da ke hanyar zuwa garin Tsaskiya. Har ilau yau, masu garkuwar sun ɗauke wata tsohuwa mai suna Dudun Bawale, wadda ke Unguwar Kudu da masu garkuwar suka maido bayan kwana ɗaya a hannunsu. Kamar yadda majiyarmu ta ce, masu garkuwar sun maido Dudu ne domin ba ita ce suka yi nufin sacewa ba.

Wadansu daliban Jami’ar Tarayya da ke Dutin-ma suna daga cikin waɗanda aka ce sun faɗa hannun barayin mutanen, labarin da hukumar jami’ar ta ce ba shi da sahihanci. Malam Bala Baidu, wanda ɗansa Shamsu ke hannun masu garkuwar ya ce, “Abin akwai tashin hankali sosai, ta kai fagen iyalina duk babu wanda yake cikin hayyacinsa saboda baƙin ciki.”

Shi dai Shamsu Bala na ɗaya daga cikin mutane ukun da aka sace, Inda ake neman Naira milIyan ɗaya kafin a sako shi. Malam Bala ya ce, “Duk wani abin amfani mun sayar da shi domin samun waɗancan kuɗi da muke sa ran ganin Shamsu a daren Larabar nan (wancan mako) amma muna da yaƙinin dawowarsa gida yau Alhamis (wancan mako).

Duk dai a cikin Karamar Hukumar Dutsin-ma, garin Dabawa da ke hanyar zuwa Katsina bai tsira daga masu garkuwar ba, domin sun yi awon gaba da Shamsu, Nomau, Sharhabila, Nasiru, Abdul’aziz da Danlami. An ce sun saki Danlami nan take bayan samun kuɗin da suka yi a wajensa har Naira dubu 300. Sauran kuwa sai an biya Naira milyan 15 kafin a sako su.

Shi kansa babban birnin Katsina bai tsira daga masu garkuwa da mutanen ba, inda faruwar haka ya sa wadansu da aka tuntuɓa suka ce ana amfani da sinadari mai ɓatar da hankali don tafiya da mutane. Kamar yadda wasu majiyoyi (ba daga hukumomi ba) suka ce, an samu wannan matsala ta sacewa don yin garkuwa a wajen Kofar Kaura, Shararrar Fiyis da Ɗaki Tara, inda ake zargin na Ɗaki Taran wani jami’in tsaro ne. Har ila yau, majiyar ta ce matar da ake zargin masu garkuwar sun sace wadda kuma take dauke da juna biyu, an gano ta a cikin wata unguwa (an sakaya suna) a yayin da masu garkuwar ke ƙoƙarin sake mata maɓoya.

Yayin da aka tuntuɓi Maigarin Tsaskiya, Alhaji Kabir Nuhu ya ce mafi yawan inda abin ya shafa ƙauyuka ne makwabtan garin da suka haɗa da Gobi, Karofi da Dokakara. Ya ce suna iya ƙoƙarinsu don ganin cewa wannan matsala ta kau tare da yin addu’o’in samun zaman lafiya.

Shi ma takwaransa na Dabawa ya ce, duk da cewa ba su da rahoton faruwar irin wannan a nan cikin gari, amma duk da haka yana bayar da shawara a kan a nemi waɗannan mutane domin a yi sulhu da su kamar yadda ake da na barayin shanu.

Shugaban Kungiyar Ci gaban Unguwar Tsamiya, Malam Sani Dutsin-ma, kira ya yi a ƙara yawan ’Yan Sintiri, waɗanda za su haɗu da jami’an tsaro domin ɗaukar duk wasu matakan da suka kamata.

Sai dai wata babbar matsalar da ke tayar da hankali ita ce, tsoro da tsoratarwar da masu garkuwar ke yi ga iyalan waɗanda suka sace. Suna hana su kai rahoto ga jami’an tsaro ko bayyana wa kafofin watsa labarai. Sukan yi musu barazarar ɗaukar mummunan mataki, inda suka aiwatar da haka in ma dai ga shi wanda ke hannunsu ko ga duk wanda ya bayyana. Wannan tsoro ne ya sa mafi yawan waɗanda abin ya shafa da ake tuntuɓa suke yin shiru ba tare da bayyana abin da ya faru ko yake faruwa ba.

A nasu ɓangaren, ’yan sanda a jihar, ƙarƙashin jagorancin Kwamishina Muhammad Wakili sun ce matsalar tana raguwa a halin yanzu in aka kwatanta da baya. Hakan kuwa ya faru ne saboda irin yadda jami’an tsaron suke ta kai samame a duk inda suka samu labarin maɓoyar masu  garkuwar ne. Kwamishinan ya ce a irin wannan samame ce suka yi nasarar kama wadansu daga cikin waɗanda ake zargi, cikinsu  har da Abdullahi Bello, wanda ake yi wa laƙabi da ‘Gemu’.

Gemu ya rasa ransa a yayin da suka yi musayar harbe-harbe da jami’an tsaro. Kwamishinan ya ƙara da cewa, bisa ga umarnin da Babban Sufeton ’Yan sanda na Kasa ya bayar na tabbatar da tsaro, tuni suka tura wasu rukunonin jami’ansu kashi uku waɗanda ke da horo na musamman a wuraren da abin ya shafa.

Ita kuma Gwamnatin Jihar Katsina ta ce tana ɗaukar duk wasu matakan da suka wajaba domin ganin an samar da tsaro a duk fadin jihar. Kamar yadda Alhaji Abdu Labaran, Mai bai wa Gwamna Shawara ta Kafafen Sadarwa ya ce, Gwamna Masari ya ce babu batun sassauci ga duk wanda aka kama. A kan haka Gwamna Masari ya umarci jami’an tsaron da ke cikin jihar su yi iya ƙoƙarinsu don ganin sun shawo kan matsalar ta hanyar inganta matakan tsaro a lungu da saƙon jihar, cewa lallai duk wanda aka kama da laifi ya fuskanci shari’a.

Kazalika, Gwamnan ya gargaɗi masu rike da sarautun gargajiya da ke yankunan da abin ya shafa da kada su sake su ba wani laifi ko wanda ake zargi wata kariya ko maɓoya. Ya ce kowa ya tsaya bisa aikinsa domin gwamnati ba za ta lamunci sakaci a kan duk wani abin da ya shafi tsaron rayuka da dukiyoyin jama’arta ba. Gwamnati a kowane lokaci tana ƙoƙarin samar da abubuwan walwala da kayan more rayuwa ga al’umarta. Gwamna Masari sai ya yi kira ga jama’a su riƙa kai rahoton duk wani ɓatagari ko wani abin da ba su amince da shi ba ga hukumomin da abin ya shafa.