✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu garkuwa da mutane shida sun shiga hannu

Sau biyu suna yin garkuwa da 'yan gida daya suna karbar kudin fansa

Wasu masu garkuwa da mutane da suka addabi dazukan Lame da Burra a Jihar Bauchi sun shiga hannu.

Bata-garin sun yi garkwa da wasu ’yan mata biyu ’yan gida daya a garin Burra inda suka karbi kudin fansa N250,000.

“Daga bisani suka dauke mahaifin yaran suka karbi Naira miliyan biyu kafin a kama su”, ijin Kakakin ’Yan Sandan jihar, DSP Mohammed Wakili.

Ya ce an kama shida daga cikin masu garkuwar ana kuma kokarin cafko wasu uku da suka tsere.

DSP Wakili ya ce an kama su ne bayan hadimin mai gidan da suka sace ya sandar da ’yan sandan abin da ya faru.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Lawan Tanko Jimeta, ya sa a titsiye wadanda ake zargin a Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar domin a gurfanar da su a kotu.