Fitaccen mahaddacin Alkur’anin nan Alaramma Ahmad Sulaiman wanda ya shiga hannun masu satar mutane shi da ‘yan uwansa biyar a hanyar Sheme zuwa Kankara a Jihar Katsina kuma suka shafe kwana 13 a hannunsu, ya shaida wa Aminiya cewa sai da aka yi musaya da mahaifiyar shugaban wadanda suka kama su, kafin a sako su, kuma ya kara bayani kan yadda rayuwarsu ta kasance a can:
Aminiya: Yaya aka yi aka sace ka?
Ahmad Sulaiman: Abin ya faru ne ranar Alhamis 14 ga Maris lokacin muna kan hanyarmu ta dawowa daga Jihar Kebbi. Akwai daurin auren ’ya’yana uku da za a yi a ranar Juma’a wato washegari. Kafin wannan lokaci ina da wata gaisuwar rasuwa da zan je a Birnin Kebbi amma saboda abin ya hada da gidan gwamnati na yi kokarin in samu iznin zuwa amma ban samu ba har sai ranar Laraba. An sanar da ni cewa matar Gwamna ta nemi in je da safe ranar Alhamis wanda hakan ya sa na tafi a wancan rana.
Motarmu ba ta da cikakkiyar lafiyar da za ta yi doguwar tafiya tunda muka tashi daga Kano muke fuskantar matsala hakan ya sa muka rika tsayawa a hanya inda muka isa Birnin Kebbi a makare. Kuma da muka tashi dawowa mun bar can a makare. Lamarin ya faru ne daidai wani gari da ake kira Kakumi kafin mu kai garin Kankara a Jihar Katsina. Ba mu yi aune ba sai muak ga wadansu mutane a cikin kayan sojoji inda suka fara harbe-harbe. A nan harsashi daya ya bugi jikin motarmu sai suka zo suka fito da mu daga cikin motar suka kwantar da mu inda suka doddoke mu tare da tattaka mu. Da farko sun karbi kudin da ke hannunmu Naira dubu 500 inda suka umarce mu da mu tafi. Daga baya kuma suka canja shawara suka tafi da mu cikin daji. Wannan ya faru misalin karfe 11 na dare. Haka muka rika tafiya a dajin nan har gari ya waye. Sannan suka kawo babur suka dauke mu suka kara kutsawa cikin dajin da mu har muka isa wani dan wuri da wasu kananan bukkoki wanda mutum ba ya iya shiga sai ya durkusa. Bayan mun shiga ciki sai suka saki harbi.
Aminiya: Su wane ne sauran mutum biyar da aka sace ku tare?
Ahmad Sulaiman: Yayana ne da ’yan uwana da sauran dangina. Haka dama muke yin tafiya.
Aminiya: Yaya za ka bayyana rayuwa a wancan wuri?
Ahmad Sulaiman: A gaskiya rayuwa ce ta firgici. A koyaushe a cikin tsoro muke domin koyaushe suna yi mana barazanar za su kashe mu idan har ba a biya musu bukatarsu ba. Sai dai da taimakon Allah da albarkar Alkur’ani ba su taba ni ba musamman shugabanninsu. Sai dai wadansu fitinannun yaransu sun sha yunkurin cin mutuncinmu domin wani a cikinsu har mari ya kwada min. Idan mutum yana son zagayawa ban-daki sai ya nemi izini. Za a raka ka tare da daga bindiga da adduna har ka gama abin da kake yi. Haka kuma ba su barinmu mu yi wanka. Amma a matsayina na shugaban mutanen an ba ni izini in yi wanka sau uku, daga baya kuma suka ce ba zan sake yin wanka ba.
Aminiya: Yaya kuke cin abinci a wancan wuri?
Ahmad Sulaiman: Da farko suna sayen abinci su ba mu, daga baya sai suka fara girlkawa. A koyaushe shinkafa da wake ne ko taliya inda za a zuba manja da dan gishiri. Sai dai lokacin da na yi korafin mafitsara sai suka rika ba ni koko shi ke nan abincina a kullum. Idan za mu shiga cikin mutum biyu ko hudu daga cikinsu za su kwanta a kofar da bindigoginsu inda kuma ake ajiye mutum kamar 8 suna gadinmu. A nan za su zauna su yi shaye-shayensu inda suke buso mana hayakin cikin bukkar da muke ciki inda suke zaginmu tare da yi mana barazanar za su kashe mu tunda mutanenmu sun ki biyan kudin fansa a kan lokaci.
Na kula da wadansu daga cikinsu suna yin abin ne ba don suna so ba, sun gaya mana cewa yawancinsu ba su da gona ba su da shanu, a cewarsu idan suka kuma shiga cikin birane ana kyararsu, hakan ya sa suka shiga wannan mummunar harka.
Aminiya: Da wane harshe mutanen suke magana?
Ahmad Sulaiman: Ni ina ganin Fulani ne domin da Fulatanci suke magana a tsakaninsu sai dai idan za su yi magana da mu ne suke yin Hausa.
Aminiya: An kyale ka kana tilawar Alkur’ani a wurin?
Ahmad Sulaiman: Kwana 12 da muka yi a hannunsu na samu damar yin tilawa daga farkon Alkur’ani har karshensa sau biyar da rabi haka kuma ina yin zikiri. A kowace rana nakan yi tilawar rabin Alkur’ani da sauran zikirori. Wannan dama ce wacce a gida ba na samunta. Ba su hana mu karatunmu har sai da ta kai suna nadamar ajiye mu da suka yi a wurinsu. A wurin ma suka shaida mana cewa ba su taba shiga tashin hankali kamar wannan lokaci ba domin har addu’a suka nemi mu yi musu don kada a kawo musu hari ko a kashe su. Ina ganin addu’o’in da jama’a suka rika yi mana da wadanda muke yi da kanmu ne suka sanya su cikin wannan hali.
Aminiya: Kuna yin Sallar farilla yadda ya kamata kuwa?
Ahmad Sulaiman: Wani lokacin ma su ne suke cewa mu fito mu yi Sallah duk da cewa su ba su yi. Wani a cikinsu yana yin Sallah tare da mu domin har roka ta ya yi in yi masa addu’a don ya daina abin da yake yi.
Aminiya: Kun samu wadansu da aka kama a wurin?
Ahmad Sulaiman: A’a ba mu hadu da kowa ba. Amma lokacin da suka fara samun rashin jituwa a tsakaninsu sai suka canja mana wuri.
Aminiya: Wacce irin rashin jituwa suka samu?
Ahmad Sulaiman: Abin da ya faru wadansu daga cikinsu sun yarda a sake mu, wadansu kuma sun ce dama ce gare su ta samun kudi. A kan haka ne aka canja mana wuri mai nisa. Sun gaya mana cewa an canja mana wuri ne saboda wadansu mutanen masu sana’a irin tasu suna so su kawo musu hari saboda mu.
Kasancewar ni ne Shugaban Kwamitin Afuwa na Jihar Kano wani ya kira su a waya ya gaya musu cewa ni ne nake da alhakin kama duk wanda ke daure a kurkuku. Wani daga cikinsu ya shigo ya same ni a cikin bukka ya zazzage ni har yana yi min barazanar zai karya min kafafuwa idan ya dawo. Saboda wannan barazanar ce suka samu matsala a tsakaninsu inda wadansu daga cikinsu suke cewa ya kamata ya kyale ni tunda ba shi ne ya kamo ni ba. Daga baya ake gaya min cewa mutum biyu a cikinsu sun rasa ransu saboda fada a kanmu.
Aminiya: A gabanka aka rika yin yarjejeniyar?
Ahmad Sulaiman: A wasu lokuta suna yin magana a gabana wani lokacin kuma ba a gabana ake yi ba. A yawancin lokuta suna yi a gabana don su tsorata mutanena domin a wasu lokutan za su ji yadda nake yin kuka saboda damuwa. Abin da yake damuna shi ne yadda mutanena suka kasa hada kudin fansar saboda ba su san hakikanin halin da nake ciki ba. A lokacin ban san cewa ana tattaunawa sosai da jami’an tsaro wadanda suka turo jami’ansu don su tserar da mu ba.
Aminiya: Yaya aka kare yarjejeniyar?
Ahmad Sulaiman: An gaya min sun ce za su bayar da Naira miliyan 33 wanda kuma kudin ba su cika ba. Sun yi mana barazaana cewa ko an biya kudin, to sai sun kashe mu saboda a dalilinmu an kama musu wani mutum. Muna nan sai muka lura sun kara firgicewa. A daren da za a sake mu suka zo wurinmu suka ce mu yi sauri mu sa takalmanmu saboda sun ji labarin wadansu mutane suna shirin kawo musu hari saboda mu. A nan aka sa wadansu mutum biyu daga cikinsu suka yi mana rakiya zuwa wani dan kauye sai dai ba wanda ya dauki makami a cikinsu da niyyar cewa idan sun tabbatar wadancan mutane ne wadanda suka yi fada da su tun farko za su nuna mana hanyar da za mu bi mu tsira. Daga baya ne muka gane cewa mutanen da suka zo su ne wadanda suka zo don su yi musayarmu da mahaifiyar shugabansu wanda aka kama saboda hakan. Haka aka kawo mu gefe daya tare da wadanda suka sace mu, a daya gefen kuma ga jami’an tsaro da suka zo da mahaifiyar shugabansu. A nan aka yi musayarmu a gaban sojoji a Danmusa da ke Jihar Katsina.
Mun samu labarin cewa mahaifiyar shugaban nasu ta shafe tsawon kwana bakwai a hannun jami’an tsaron, saboda lokacin ta musanta cewa shi din danta ne. To ta haka ne muka samu ’yancinmu.
Aminiya: Me kake tunanin ya kamata gwamnati ta yi don magance wannan matsala?
Ahmad Sulaiman: Akwai bukatar gwamnati ta zauna ta tattauna da shugabanninsu ta kuma sama musu abin da suka ce ba su da shi na noma da kiwo. Ina ganin idan aka yi haka abubuwa za su canja.