Wata kididdiga da kafar Statisense ta fitar a shekarar 2024 da muke bankwana da ita ta nuna cewa mawaƙin Najeriya Wizkid ne ɗan Afirkan da aka fi ambato a shekarar 2024.
Kafar ta rairayo mutum 30 wadanda bincikensu ya gano cewa an fi magana a kansu a shekarar.
Mutanen sun hadar da shahararren mawakin nan Wizkid da Davido da Tyla da attajiri Alhaji Aliko Dangote da sauransu. Ga bayanin biyar daga cikinsu:
1- Wizkid
Shahararren mawakin Afrobeats na Najeriya Ayodeji Ibrahim Balogun wanda aka fi sani da Wizkid shi ne mutum na farko da a jerin sunayen da Statisense ta gabatar a matsayin mutumin da aka fi ambaton sa a 2024.
- Gwamnatin Kano ta raba wa waɗanda gobara ta shafa tallafin N12.7m
- An kashe abokin ango a taron ɗaurin aure
- Ra’ayoyin ’yan Najeriya kan tashin Matatar Warri
Aminiya ta gano cewa dalilan da Wizkid ya fi shahara a mutanen da aka fi ambatonsu a 2024 sun hada da bayan sabon sabani da ya samu da Davido da kuma sakin sabon album ɗinsa mai suna ‘Morayo.’
Sai kuma sabuwar motar alfarma kirar McLaren 750S da ya saya kan kudi kimanin Naira bilyan 1.5. Bidiyoyin yadda ya zagaya cikin sabuwar motar a birnin Legas ya kara jan hankalin dinbin magoya bayansa.
2- William Ruto
Shugaban Kenya William Ruto ya yi fice a shekarar 2024 saboda wasu muhimman matakai da ya dauka kasar. A watan Yuni ne shugaban ya sallami duk ministocinsa bayan wata zanga-zangar da ’yan kasar suka gudanar domin nuna adawa da sabuwar Dokar Haraji da ya gabatar.
Shugaban ya janye kudirinsa na ƙarin kuɗin harajin bayan matsin lambar da ya sha daga masu zanga-zangar wanda takai ga sun kutsa har cikin zauren Majalisar Dokokin kasar, tare da yin barazanar ci gaba da ɗaukar ƙarin wasu matakai na nuna adawa da shirin, muddin shugaban ya yi gaban kansa wajen sanya wa dokar hannu.
Ruto ya tattauna da matasan da ke jagorantar zanga-zangar sannan ya rage kasafin kudin fadar shugaban ƙasar da naɗa sabbin ministoci ciki har da ’ya adawa don kafa gwamnati mai faɗi.
3- Davido
Mawaki Davido shi ma kamar Wizkid a 2024 yana daya daga cikin mutanen da aka fi ambata a Afrika.
Duk da kasancewarsa mawakin shahararre a duniya, bikin daurin aurensa a amaryarsa Chioma da aka shafe kwanaki ana yi, yana daga cikin dalilan da suka sa aka yawaita ambatonsa a shekarar.
Davido shi ne ya zo na hudu a jerin sunayen da kafar statisense ta gabatar. Davido ba tun bana ba ya kasance mawaki mai dimbin magoya baya kuma a 2024 tauraruwarsa ba ta disashe ba, ya ci gaba da zama cikin jerin wadanda suka haska a shekarar.
4- Bola Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, shi ne mutum na hudu a jerin. Tinubu, tun bayan karbar mulkinsa a 2023 ya shiga bakin musamman ‘yan kasar saboda tsauraran sauye-sauyen gwamantinsa a bangaren tattalin arziki da siyasa da sauransu.
A tsakaanin wata 18 da Tinubu ya yi ya samar da sabbin dokiki kamar na cire tallafin mai da wutar lantarki; zare wani kaso na kudin makarantar daliban da ke karatu a gaba da sakandire, da sauya taken Najeriya, da kuma kwana-kwanan, nan gabatar da kudirin sabuwar dokar haraji wacce ta janyo muhawara mai zafi tsakanin al’umma.
5- Aliko Dangote
Alhaji Aliko Dangote, attajirin Najeriya da Afirka, kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana a jerin attajirai 40 na nahiyar shi ne mutum na biyar da kididdigar statisense ta yi.
Dukiyar Dangote ta ninku tun bayan fara aikin matatar man da ya samar a Legas, duk da cewa an samu tangarda tsakaninsa da mahukunta a Najeriya da kuma matatar.
Dangote ya yi tashe sosai tun bayan fara aikin matatar da irin dambarwar da aka sha tsakaninsa hukumomin gwamnati da suka danganci nagartar man da matatar ke tacewa da batun farashi da kuma kasuwancin man da uma yadda zai samu danyen mai, kafin daga karshe a sasanta.
Wasu
Matatar Dangote wacce ta kasance mafi girma a Afirka an kashe kudi dala biliyan 20 a wajen gina ta a Legas kuma an sa ran za ta kawo ƙarshen dogaron da Najeriya ke yi da ma
n fetur da ake shigowa da shi daga waje har ma da tallafa wa maƙwabtan ƙasashe.