✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abba ya sanya hannu kan kasafin kuɗin N719bn na 2025

Gwamnan ya cw kasafin zai mayar da hankali wajen bunƙasa tattalin arziƙin jihar.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2025 na Naira biliyan 719.

A ranar 8 ga watan Nuwamba, 2024, Gwamnan ya gabatar da kasafin kuɗi na Naira biliyan 549.76 ga Majalisar Dokokin Jihar.

Majalisar ta amince da ƙarin kasafin kuɗin na Naira biliyan 719.76 biliyan, bayan ta yi ƙarin Naira biliyan 170 a kai.

Shugaban majalisar, Jibril Ismail Falgore, ya bayyana cewa jimillar kuɗaɗen da ake sa ran samu a shekarar 2025 zai kai Naira 549.16 biliyan.

Hakazalika, ya ce ana sa ran samun Naira biliyan 75.72 biliyan daga cikin gida.

Wannan na nufin kimanin kashi 13.8 na kuɗaɗen da ake sa ran samu, yayin da sauran kashi 86 zai fito daga Asusun Tarayya da sauran hanyoyin samun kuɗaɗe.

An amince da kasafin kuɗin da ya haɗa da Naira biliyan 262.67 wanda za a kashe kuɗaɗen yau da kullum (kashi 36) da Naira biliyan 457.08 na ayyukan ci gaba (kashi 64).

Gwamnan ya bayyana kasafin kuɗin a matsayin “Kasafin Kuɗin Ilimi, da Ci gaban Tattalin Arziƙi.”

Kasafin kuɗin zai mayar da hankali kan inganta ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa, samar da ruwa, ci gaban ƙauyuka, tsaro, rage talauci, noma, da ci gaban tattalin arziƙi.

Bayan sanya hannu kan kasafin kudin, Gwamnan ya jaddada cewa zai taimaka wajen taimaka wa jama’a, ƙara bunƙasa tattalin arziƙi, da magance talauci, musamman a tsakanin matasa.

Ya gode wa Majalisar Dokokin Jihar Kano, bisa jajircewarsu da kuma aikin da suka yi wajen amincewa da kasafin kuɗin.