Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga ’yan Najeriya su zama masu haɗin kai tare da tabbatar da cewa shugabanni na ɗaukar nauyin da ya rataya a wuyansu.
A wata sanarwa da ya sanya wa hannu kuma ya raba wa ’yan jarida a ranar Talata, Atiku ya bayyana 2025 a matsayin shekarar da za a samu waraka.
- Abba ya sanya hannu kan kasafin kuɗin N719bn na 2025
- Gwamnatin Borno ta horar da mata 162 sana’o’in dogaro da kai
Ya buƙaci ’yan Najeriya su kasance masu kula da abin da shugabanni ke yi a kowane mataki.
Ya ce sabuwar shekarar zai ta bai ’yan ƙasa damar yin sake nazarin yadda ake tafiyar da al’amuran ƙasar, tare da kare dimokraɗiyya ta hanyar tabbatar da shugabanni sun zama masu gaskiya.
Atiku, ya jaddada wahalhalun da aka fuskanta a 2024, inda ya gode wa Allah da ya bai wa ’yan Najeriya damar ganin wata sabuwar shekarar.
Ya ce ƙalubalen da aka fuskanta a baya za su ƙarfafa haɗin kai da imani a tsakanin al’umma.
“Wahalhalun shekarar da ta gabata sun ƙara mana ƙarfin gwiwa da kariyar Allah,” in ji shi.
“Wannan zai ci gaba da zama fatanmu yayin da muke burin samun ci gaba.”
Atiku, ya yi kira ga ’yan Najeriya su haɗa kai don samar da makoma mai kyau kuma su tabbatar da cewa shugabanni ba su yin amfani da ikon da aka ba su wajen cin amanar jama’a ba.
Ya kuma gargaɗi gwamnati kan yin duk wani abu da zai tauye w haƙƙoƙin jama’a.
Haka kuma, Atiku ya yi addu’ar samun ci gaban tattalin arziƙi a 2025, tare da fatan samun sauƙi daga mawuyacin halin tattalin arziƙin da ya dabaibaye ƙasar.