Wadanda suka yi garkuwa da mambobin cocin Living Faith da ke yankin Osara a Karamar Hukumar Adavi a Jihar Kogi sun bukaci a ba su miliyan uku a matsayin kudin fansa.
Aminiya ta rawaito yadda maharan suka shiga cocin da ke kan titin Lokoja zuwa Okene suka yi awon gaba da mutum uku daga cikin masu ibada a cocin.
- Yadda ‘Yan Siyasa “Ke Mayar Da Matasa ‘Yan Kwaya”
- Abubuwan da suka faru har Taliban ta karbe Afghanistan
Daya daga cikin iyalan wadanda aka sace din da ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana wa wakilinmu ta wayar tarho cewa tun ranar Litinin maharan suka kira waya suka bukaci miliyan daya a kan kowane mutum da suka sace.
Ya ce sun roki maharan a kan su rage kudin fansar, suka kuma bayyana musu cewa wadanda aka sace din masu karamin karfi ne duba da yadda suke shan wahala sakamakon halin da ake ciki a kasar nan.
“Gaskiya, an yi magana da su a ranar Litinin, sun bukaci miliyan daya kan kowane mutum kafin su sake shi. Amma iyalansu na neman ragi saboda yanayin da ake ciki a kasa,” a cewarsa.
Sai dai ya ce da iyalan ke neman ragi, sai masu garkuwar suka kashe wayarsu.
Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Williams Ovye Aya, bai amsa kiran waya ko rubutaccen sakon da wakilinmu ya tura masa ba don jin ta bakinsa game da lamarin.