✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Masu garkuwa da Kwamishinana za su fuskanci tsattsauran hukunci’

Gwamnan ya ce gwamnatin Bayelsa za ta sa kafar wanda daya da masu satar mutane.

Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri ya ce zai tabbatar da cewar an yi duk abin da ya dace wajen ganin an ceto Kwamishinansa, Mista Oparniola Otokito, da wasu mahara suka sace a makon da ya wuce.

Gwamnan ya ce dole ne wanda suka yi garkuwa da Kwamishinan su sake shi ko kuma gwamnati ta tabbatar da sun fuskanci tsattsauran hukunci.

An yi garkuwa da Mista Otokito, wanda Kwamishinan Harkokin Kasuwancin Jihar ne a ranar Alhamis a gidansa da ke yankin Otuokpoti a Karamar Hukumar Ogbia ta Jihar.

Kazalika, Gwamnan ya ja kunnen matasan jihar da su kaucewa aikata muggan laifuka da suka hada da garkuwa da mutane da sauransu.

“Na bar Yenagoa zuwa Abuja sai aka samu wasu suka sace daya daga cikin mukarrabaina. Mutane da dama na zuba idon zan yi jawabi ko fitar da sanarwa, amma su sani ni ba mutum ne mai yawon babatu ba.

“Ina ba wa wanda suke garkuwa da mutane a Bayelsa shawarar cewar su tuba su daina tun lokaci ba kure musu ba, saboda akwai doka a Bayelsa kuma za ta yi aiki a kan su.

“Ina nan ina ci gaba da yin duk abin da ya dace don ganin an tseratar da shi cikin koshin lafiya ba tare da an bari wanda suka sace shi sun cutar da shi ba,” a cewarsa.