Wadanda suka yi garkuwa da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Neja, Muhammad Sanni Idris, sun bukaci a ba su Naira miliyan 500 a matsayin kudin fansarsa.
Aminiya ta rawaito cewa an sace Kwamishinan ne a mahaifarsa da ke Babban Tunga a Karamar Hukumar Tafa ta Jihar, da sanyin safiyar Litinin.
- Lissafi ya fi kowane darasi sauki – Malamin jami’a
- Abin da ya sa zan gina jami’ar Musulunci a Daura – Rochas Okorocha
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu a Minna, babban birnin Jihar cewa tuni ’yan bindigar suka fara tuntuba ta waya domin a fara ciniki.
“Suna neman a ba su N500m, yayin da taron majalisar tsaron Jihar da Mataimakin Gwamnan ya jagoranta bai jima da kammala ba a Gidan Gwamnati, amma babu cikakkun bayanai a kai,” inji majiyar.
Rahotanni sun ce tun da safe ake ta taro kan matsalar tsaro a Jihar.
Sai dai har yanzu babu wani tabbaci a hukumance daga gwamnati kan bukatar ’yan bindigan.