✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu garkuwa da dan shekara 3 na neman kudin fansa na N2m

Sun yi barazanar cewa yana iya rasa ransa idan aka gaza biyan kudin fansar.

Al’ummar garin Potiskum a Jihar Yobe sun shiga rudani bayan samun rahoton cewa wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wani yaro dan shekara 3 da haihuwa mai suna Adamu Abubakar Baban Yawo.

Labarin hakan ya fito ne a wata takardar da ’yan sanda suka raba wa manema labarai.

’Yan sun bayyana cewa yaron yana wasansa ne a kofar gida tare da wansa Mohammad Abubakar a yayin da wasu mutane 3 da ba a san su ba suka yi awon gaba da shi.

Takardar ta bayyana cewa ’yan bindigar da suka sace yaron sun kira iyayensa ta wayar salula suna neman a basu Naira miliyan 2 a matsayin kudin fansa.

Har ila yau, takardar ta ce masu garkuwa da yaron sun yi barazanar cewa yana iya rasa ransa idan aka gaza biyan kudin fansar da suka nema.

A halin yanzu dai ana zargin cewa masu garkuwa da yaron suna da kusanci da iyayen yaron.

Wakilinmu ya ruwaito mazauna gari na mamakin yadda masu garkuwar suka samu lambar iyayen yaron har suka kira, suna masu cewa hakan  ma abun tuhuma ne saboda yaron bai da waya.

Iyayen dai suna neman jama’a da su taya su rokon Allah Ya kubutar musu da dansu cikin koshin lafiya.