✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu garkuwa da Babban Sakatare a Neja na neman N60m

Sai dai bayan dogon cinki, sun amince a basu N30m.

Masu garkuwa da Babban Sakataren Ma’aikatar Sufuri ta Jihar Neja, Dokta Ibrahim Musa Garba sun bukaci a basu Naira miliyan 60 a matsayin kudin fansarsa.

An dai sace shi ne tare da wata ’yarsa mai kimanin shekara uku a ranar Juma’a yayin wani daurin aure da aka yi a gidansa da ke Zungeru a Karamar Hukumar Wushishi ta Jihar ta Neja.

Wani makusancin iyalin da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa masu garkuwar sun kira waya da yammacin Lahadi, inda suka bukaci a basu adadin kudin kafin su sake shi tare da ’yar tasa.

Ya ce, “Ranar Lahadi da yamma sun kira iyalansa ta waya suna neman a basu Naira miliyan 60. Amma bayan an yi dogon ciniki, sun yi ragi inda suka amince akan Naira miliyan 30.

“Amma maganar gaskiya ita ce iyalansa basu da wannan kudin. Za mu ci gaba da neman ragi duk lokacin da suka sake kira,” inji shi.

Daga nan sai ya yi kira ga Gwamnatin Jihar ta Neja da ta taimaka musu wajen ceto mutumin tare da ’yar tasa ba tare da an cutar da su ba.