Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya mai da martani kan jita-jitar da wadansu ke yadawa cewa shi jabu ne an sauya shi ne da wani mai kama da shi bayan ya rasu a lokacin da yake jinya a Landan a bara.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da wadansu ’yan Najeriya mazauna kasar Poland a ranar Lahadin da ta gabata a birnin Krakow inda ya ce, lallai shi ne Buhari na ainihi da aka sani ba na boge ba.
Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayar wani daga cikin ’yan Najerjya mazaunin kasar, inda ya nemi ya san ko da gaske shi ne ainihin Buhari ko kuma wani mutum mai suna Jubril al-Sudani daga kasar Sudan da ake zargin yana basaja a matsayin Shugaban Kasar.
Shugaba Buhari ya bayyana cewa, lallai masu yada wannan magana jahilai ne marasa addini, “Mutane da yawa sun yi fata a ce na mutu a lokacin da na yi rashin lafiya kwanakin baya, wadansu da yawa ma sun fara tuntubar Mataimakin Shugaban Kasa, suna neman ya nada su a matsayin Mataimakin Shugaban Kasa in har an tabbatar da mutuwata. Abin ya tayar masa da hankali kwarai da gaske, har sai da ya ziyace ni a asibiti a Landan. Ina tabbatar muku da cewa ni ne. Kuma kwanan nan ma zan yi bikin cika shekara 76 da haihuwa. Kuma ina nan da karfina,” inji Buhari.
Shugaban Kasar ya kuma bayyana cewa, “Wannan tsangwamar da ake yi mini, jikokina ne lamarin ya fi daga wa hankali.”
Daga nan sai ya ce, gamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da ginshikan alkawura da ta yi lokacin yakin neman zabe da suka hada da samar da tsaro da inganta tattalin arziki da kuma uwa uba yaki da cin hanci da rashawa.
“Mutanen da suke yankin Arewa maso Gabas sun san cewa, duk da matsalolin da ake fuskanta a ’yan kwanakin nan, abubuwa sun canja idan aka kwatanta da lokutan baya. “Lallai an samu ci gaba kwarai a fannin samar da tsaro da tattalin arziki. A halin yanzu mun daina shigo da kayan abinci musamman abin da ya shafi shinkafa, hakan kuma ya sa mun yi tattalin kudade masu yawa.
Shugaba Buhari yana halartar taron Majalisar Dinkin Duniya a kan canjin yanayi ne a kasar ta Poland, wanda aka yi wa lakabi da ‘UN Climate Change Conference, COP24.’ Kuma ya tabbatar da cewa, babu wani yanki na Najeriya da ke hannu ’yan ta’addan Boko Haram. Ya yi kira ga ’yan Nijeriya su ci gaba da ba gwamnatinsa goyon baya don a tabbatar da kare rayuwa da dukiyoyin al’ummar kasar baki daya a duk inda suke.