✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu fasakwaurin shinkafa sun kai wa jami’an tsaro hari

Mutum 2 sun rasu, wasu sun jikkata a fada tsakanain jami’an tsaro da masu fasakwaurin shinkafa.

Akalla mutum 2 sun rasu, wasu da dama sun jikkata a wata musayar watar da sojoji da jami’an kwastam suka yi da masu fasakwaurin shinkafar waje.

Bata-garin sun bude wa jami’an tsaro wuta ne bayan jami’an kwastam sun kama buhu 320 na shinkafar waje da aka boye a wani kango bayan an yi fasakwaurin zuwa Najeriya.

Jami’an na cikin aikin kwashe shinkafar ce masu fasakwarin da wasu ’yan daba suka bude musu wuta, su kuma suka mayar da martani tare da bindige mutum biyu daga cikin maharan, wasu da dama kuma suka samu raunuka.

Wani soja da jami’an kwastam hudu, da fararen hula biyar sun samu raunukan harbi a dauki ba dadin, da aka yi a yankin Oja-Odan da ke Karamar Hukumar Yewa ta Arewa ta Jihar Ogun.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a, kakakin Hukumar Kwastam na yankin, Hammed Oloyede ya ce “an kai wadanda suka samu raunin asibiti kuma suna samun sauki.”

 A cewarsa, duk da harin da aka kai musu, jami’an sun kwashe haratattun kayan, suka kuma kama babura shida da wani mutum da ake zargin da fasakwaurin kayan.

“Ana gudanar da bincike domin gano sauran masu hannu a aika-aikan… hare-haren da masu fasa-kwauri ke kai wa jami’anmu ba zai sa su yi kasa a gwiwa wajen sauke nauyin da ke wuyansu ba.

Ya kuma bukaci sarakunan gargajiya da shguabannin al’umma da su gargadi mabiyansu su guji kai wa jami’an tsaro hari, domin duk wanda aka kama zai yaba wa aya zaki.