Akalla jami’an kwastam uku da soja daya ne suka ji munanan raunuka bayan masu fasa-kwaurin shinkafa sun bude musu wuta.
Kakakin Hukumar Kwastam Shiyya ta Daya, Theophilus Duniya, ya sanar da manema labarai a birnin Ibadan cewa lamarin ya faru ne a yankin Igboora na Karamar Hukumar Ibarapa ta Jihar Oyo.
- Dubun masu satar yara a akwatin gawa ta cika
- Ya jagoranci kai farmaki kayukan Zamfara saboda kama mahaifinsa
“Jami’an kwastam da ke aiki sun hangi tirela takwas dauke da shinkafar da aka yi fasa-kwaurinta, amma nan take direbobin motocin suka farmake su.
“An harbe daya daga cikin wadanda suka farmaki jami’an tsaron an kuma kwace makaminsa, ragowar kuma sun tsere.
“Ana ci gaba da binciken wadanda suka kai harin don gurfanar da su a gaban kuliya, dukkannin jami’an da suka ji rauni, ciki har da soja daya kuma suna samun kulawa,” a cewar Duniya.
Ya ce DC Usman Yahaya, ya yi Allah wadai da harin, tare da ba da tabbacin cewa hukumar za ta ci gaba da yakar masu fasa-kwaurin shinkafa a fadin Najeriya.
A cewarsa, daukar makamai da wasu bata-gari ke yi ba zai hana jami’an hukumar yin aikinsu ko yakar masu fasa-kwaurin shinkafa ba.